An cafke bokan da ke hadawa 'yan ta'adda a arewa tsafi da sassan jikin mutane

An cafke bokan da ke hadawa 'yan ta'adda a arewa tsafi da sassan jikin mutane

- Runduna sojin Najeriya ta musamman ta sanar da nasarar da ta samu wurin cafke kungiyar asirin Gana

- Ta bayyana hakan a ranar Laraba yayin da dakraun suka cafke mutum 41 da ke da alaka da Gana

- Kwamnadan kungiyar ya nuna farincikinsa yayin sanar da kamen tare da cewa suna cigaba da neman miyagun

Runduna ta musamman ta sojin Najeriya, ta yi nasarar cafke shugaban matsafar kungiyar asiri ta Gana, Mr. Ugba Iorlumun, wanda ake zargi da kashe tare da amfani da sassan jikin mutum don tsafi.

Kwamandan runduna ta musamman ta 4, Maj.-Gen. Gadzama, ne ya bayyana haka ranar Laraba a garin Lafiya yayin da ya ke holin yan kungiyar asirin Gana su 41 tare da masu garkuwa 25 da kuma yan fashi da makami.

An cafke bokan da ke hadawa 'yan ta'adda a arewa tsafi da sassan jikin mutane
An cafke bokan da ke hadawa 'yan ta'adda a arewa tsafi da sassan jikin mutane. Hoto daga @Vangaurdngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugabanci ba wasa bane: Gwamna Badaru ya gargadi masu yi masa adawa, ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri

A ta bakin Kwamandan ya ce "Ina mai matuƙar farin ciki sanar da ku cewa, yan kungiyar asirin Gana su 41 suna hannunmu. Adadin da ya kai su 119 da muka baza komar nemansu.

"Kafin wannan lokaci, babban laifi ne ka ambaci sunan Gana cikin ƙabilar Tiv, Jukun ko ta Kuteb saboda tsoron mutanen sa na iya kamo mutum su kai masa ya dafa."

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Borno ta bankaɗo malaman bogi da ma'aikatan ƙananun hukumar dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma'aikata da malamai da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da umarnin aiwatarwa.

Alƙaluman sun nuna kimanin ma'aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananun hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi.

Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ɓangaren malaman firamare kaɗai dake ƙananun hukumar 27 dake faɗin jiha.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel