Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware

Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware

- Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya sha wani alwashi tare da saka kudi $20,000

- Ya bukaci hadimin shugaban kasa, Malama Garba Shehu da ya kwana daya a Koshobe ko Kware shi kuwa zai ba shi $20,000

- Hadimin shugaban kasan ya zargi Omokri da wawuro kudin da ake hadawa don samun 'yancin Leah Sharibu don bada wa, wanda yace baya so

Reno Omokri, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sha alwashin bai wa Garba Shehu kyautar $20,000 idan har ya kwana a Koshobe ko Kware.

Omokri ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

Ya ce ya saka wannan kudin ne saboda Shehu ya ce Buhari ya tabbatar da cewa ya inganta tsaron kasar nan. Omokri ya nada Dele Momodu a matsayin shaida.

Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware
Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware.Hoto daga @renoomokri
Source: Twitter

KU KARANTA: Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari

Koshebe da Kware wurare ne a jihohin Borno da Zamfara kuma an tabbatar da cewa suna cikin wurare da rashin tsaro ya tsananta kuma hare-haren 'yan Boko Haram da 'yan Bindiga ya yi kamari.

Omokri ya wallafa, "Garba Shehu ya ce janar Buhari ya inganta tsaro a Najeriya. Na yi alkawarin bai wa Garba Shehu $20,000 idan yayi kwana daya a Koshobe ko Kware. Dan jarida mai zaman kansa Dele Momodu ne zai zama shaida in har Garba ya amince zai je."

A yayin martani ga wannan alwashin, Garba Shehu ya ce wannan kudin da Omokri ya saka yana daga cikin wadanda ya samu wurin gangamin bukatar a sako Leah Sharibu.

KU KARANTA: Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara

Shehu ya yi martani, "Idan har wannan kudin yana daga cikin wadanda ka karba domin gangamin sako Leah Sharibu, ba zan taba su ba. Adana $20,000."

A yayin nuna amincewarsa, Dele Momodu ya ce, "matukar Garba Shehu ya karba wannan kalubalen kuma ya amince da tayin Reno Omokri, tabbas zan sanar da wanda yayi nasara."

A wani labari na daban, wata matar aure ta wallafa labarinta mai cike da taba zuciya. Ta bada labarain yadda 'yar uwarta makusanciya ta koma kishiyarta dare daya.

A kokarinta na bai wa wata kwarin guiwar shawo kan matsalar aurenta, ta bada labarin yadda ta yi haihuwa ta biyu amma saboda rashin uwa, sai 'yar uwarta ta je mata zaman jego.

Kamar yadda ta bayyana, bayan isowar 'yar uwarta, sai ta fara wata boyayyar alaka da mijinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel