Karo na biyu: Ba za mu rufe Plateau ba, in ji Lalong

Karo na biyu: Ba za mu rufe Plateau ba, in ji Lalong

- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya magantu kan barkewar annobar korona a karo na biyu

- Lalong ya bayyana cewa ba zai rufe jihar ba a matsayin matakin dakile cutar

- Sai dai ya takaita yawan mutanen da za su halarci taro ciki harda wuraren bauta zuwa mutum 50

Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau a ranar Laraba ya ce bai da niyan rufe jihar a matsayin matakin dakile yaduwar annobar korona karo na biyu, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Laraba, a garin Jos yayin wata hira da masu ruwa da tsaki ciki harda shugabannin kananan hukuma, sarakuna, shugabannin addinai, hakimai da kwararru a fannin lafiya don tattauna yadda za a magance lamarin.

A wata sanarwa daga daraktan harkokin labarai da jama’a, Mecham Makut, ya ce sakataren gwamnatin jihar kuma Shugaban kwamitin korona a jihar, Farfesa Danladi Atu ne ya jagoranci taron wanda gwamnan ya shirya.

Karo na biyu: Ba za mu rufe Plateau ba, in ji Lalong
Karo na biyu: Ba za mu rufe Plateau ba, in ji Lalong Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A yayin taron, Atu ya ce an shirya taron ne don janyo hankalin masu ruwa da tsaki don magance annobar cikin gaggawa, musamman a lokacin Kirsimeti.

KU KARANTA KUMA: Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu

Ya ce gwamnan ya yi umurnin daukar tsatsauran matakai don tabbatar da ganin cewa an wayar wa da mutane kai don kiyaye dokokin korona tare da kakkabe yaduwar annobar.

Ya bayyana cewa bayan tattaunawa, taron sun dauki matakai kan korona wanda yayi umurnin zabtare yawan masu zuwa taro ciki harda wuraren bauta zuwa 50.

A cewarsa, taron ya kuma haramta duk wani biki na al’ada sannan ya kafa dokar amfani da takunkumin hanci a dukkanin taron jama’a da kuma yin nesa-nesa da juna.

Kan tsaro, sakataren gwamnati ya ce rahotannin tsaro da gwamnati ta samu ya nuna cewa wasu bata gari na shirin kai hare-hare a kan wasu garuruwa a lokacin bikin Kirsimeti.

KU KARANTA KUMA: Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello

Ya ce gwamnan ya bukaci taron da su dauki matakan lura don taimakawa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani don magance duk wani hari da miyagun za su kai.

A wani labarin, alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.

Mutane 999 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 22 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 79,789 a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng