Duba cikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan mai AC, wurin caji da bandaki kayatacce
- Wani kwastoma ya bayyana yadda jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya janyo cece-kuce da jinjina a kasar nan
- Kamar yadda mutumin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ana siyan tikitin 2,500 kuma ana samun matukar natsuwa
- A yayin da jama'a da dama suke cewa tikitin ya yi tsada, wasu na ta jinjinawa wannan cigaban da zai maye gurbin tituna
Yanayin tsarin sufurin Najeriya zai iya zama mai inganci a yadda aka fara kaddamar da jiragen kasa.
Jiragen kasa da za su dinga yawo daga Legas zuwa Ibadan a saukake ba tare da tunanin cunkoso ko lalatattun tituna ba abun dadi ne.
A wata wallafa da wani ma'abocin Twitter mai suna @dmIdavies yayi a ranar Talata, 22 ga watan Disamba, ya bayyana yadda ya hau jirgin kasa da kuma yadda ya tarar da shi.
KU KARANTA: Ke kadai kika yi dawainiyata har na kawo haka, mai bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyarta (Bidiyo)
Kamar yadda ya wallafa tare da hotunan tikitinsa, daga tashar Yaba a Legas zuwa Moniya da ke Ibadan ana karbar N2,5000.
Ya ce akwai tarin natsuwa a cikin jirgin kasan don har da AC wanda dole mutum ya ce a rage masa rabarsa akwai.
KU KARANTA: Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala
Akwai wuraren caji inda ko aiki ne mutum zai iya farawa kafin isa ofishinsa. Ya ce akwai abubuwa da yawa masu matukar inganci.
Akwai inda jirgin ke tsayawa a Abeukuta a kan hanyarsa ta zuwa Ibadan, hakan yasa tafiyar take zama ta tsayin sa'o'i biyu da rabi.
Jirgin kasan yana aiki ne sau daya a kowacce rana, yana barin Ibadan zuwa Legas da karfe 8am ya isa da karfe 10:30am sannan ya koma Ibadan daga Legas da karfe 4pm zuwa 6:30pm.
Domin samun tikitin, ana baukatar shaidar mutum amma a halin yanzu ba a yi ta yanar gizo.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga ganawar sirri da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yawaitar garkuwa da jama'a.
Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi bayani ga manema labarai bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Katsina.
Ya yi kira ga takwarorinsa da su dauka salon da za su sa matasa su gujewa aikata laifuka, jaridar The Punch ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng