Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala

Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala

- Ofishin ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ya ki magana a kan sakin Bala

- Wata kotun tarayya ta bada umarnin sakin matashin da yayi batanci ga Annabi kuma a biya shi diyya

- Kamar yadda alkalin ya bukata, a biya Bala N250,000 na diyyar hakkokinsa da aka take a watannin da yayi a tsare

Ofishin Antoni janar na tarayya sun kasa martani a kan halin da ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar Zamani na Facebook, Mubarak Bala yake ciki.

Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bada umarnin sakin Mubarak Bala bayan watannin da ya kwashe a tsare.

Sakon da aka aike wa antoni janar na tarayya bai samu martani ba har a lokacin rubuta wannan rahoton.

Amma kuma, Dr Umar Gwandu, hadimin AGF a fannin yada labarai, ya sanar da Daily Trust cewa har yanzu ofishin bai yanke shawara a kan wannan cigaban ba.

Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala
Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari

Hakazalika, kakakin rundunar 'yan sanda Najeriya, CP Frank Mba bai dauka kiran da aka dinga yi masa ba.

A ranar Litinin, Mai shari'a Inyang Ekwo ya yanke hukuncin cewa tsare Bala ya take hakkinsa na 'yanci, 'yancinsa na tunani, 'yancinsa na bayyana ra'ayinsa da kuma 'yancinsa na zirga-zirga.

Mai shari'ar ya kara da yanke wa 'yan sanda diyyar N250,000 wanda tace ta biya Bala.

An kama Bala tare da tsaresa a ofishin 'yan sanda da ke Gbasawa a jihar Kaduna kuma an mayar da shi Abuja a ranar 28 ga watan Fabrairun 2020 bayan wasu jama'ar Kano sun kai korafin batanci da yake yi wa fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa

A wani labari na daban, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i (ASUU) a ranar Talata, 22 ga watan Disamban 2020, ta bada satar amsa a kan lokacin da za ta kawo karshen yajin aikinta na watanni 9.

Kungiyar ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter. Kamar yadda wallafa ta ce: "Labari mai dadi. Za a janye yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta biya dukkan albashin da malamai ke bin ta."

A yayin magana a kan komawa makaranta, ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da ASUU sun kai kashi 98 na fahimtar juna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel