Ke kadai kika yi dawainiyata har na kawo haka, mai bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyarta (Bidiyo)
- Bidiyon wata matashiya mai hidimtawa kasa tare da mahaifiyarta ya saka jama'a hawaye
- A bidiyon, an ga budurwar ta dawo daga sansanin bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyar
- Ta sanar da yadda ta raineta, tarbiya da biya mata kudin makaranta har ta kai matsayin nan
Wata matashiyar budurwa mai hidimar kasa ta sa mahaifiyarta hawaye bayan wani jawabi mai ratsa zuciya da ta yi yayin da ta dawo daga sansanin masu hidimar kasa.
Matashiyar mai bautan kasan sanye da cikakkun kayan hidimar kasa, ta tattaka har zuwa gaban mahaifiyarta inda ta yi mata jinjina.
Kamar yadda matashiyar tace: "Jinjina kashi uku ga mahaifiyata wacce ita kadai ta raine ni, ta yi min tarbiya tare da tura ni makaranta har na kai matsayin hidimtawa kasata."
Muryar budurwar mai hidimar kasa tana rawa yayin da take jinjina ga mahaifiyarta. Mahaifiyar kuwa fuskarta dauka da hawaye wadanda aka ga tana ta kokarin gogewa a bidiyon.
A lokacin da matasiyar budurwa ta kammala, sai mahaifiyar ta rungumeta.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa
KU KARANTA: Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari
A wani labari na daban, wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta bada umarnin damko fitaccen mawakin shugaban kasa Buhari, Dauda Kahutu Rarara.
Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda yake shugabantar shari'ar, ya bayar da umarnin damko fitaccen mawakin sakamakon rashin bayyanarsa a gaban kuliya don kare kansa daga zargin da ake masa.
Tun dai daga farko, alkalin ya aika wa mawakin sammaci tare da bukatar ya bayyana a ranar 22 ga watan Disamban 2020.
Ana tuhumarsa da boye wata matar aure ba bisa ka'ida ba. Wani mutum mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya kai karar mawakin kotun domin neman hakkinsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng