'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa

'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa

- 'Yan bindiga sun halaka dan sanda bayan ya je ceton wasu da aka yi garkuwa da su a Jigawa

- Mummunan lamarin ya auku ne a kauyen Bosuwa da ke karamar hukumar Maigatari ta jihar

- 'Yan bindiga sun sace tsoho mai shekaru 70 tare da wata budurwa mai shekaru 25 a duniya

A ranar Litinin ne 'yan bindiga suka kashe jami'in dan sandan da ke kokarin ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su a kauyen Bosuwa da ke karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels TV a ranar Talata.

Ya yi bayanin cewa, bata-garin sun sace wani Ali Dankoli mai shekaru 70 a duniya da wata Zainab Isah, wacce diya ce wurin tsohon shugaban karamar hukumar Maigatari, Isa Zakari Bosuwa.

'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa
'Yan bindiga sun kashe dan sandan da ya je ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Jigawa. Hoto daga @ChannelsTv
Source: Twitter

KU KARANTA: Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m

"Yan sanda da ke Maigatari sun samu kiran gaggawa a kan cewa wasu miyagun 'yan ta'adda dauke da miyagun makamai sun tsinkayi kauyen Bosuwa da ke Maigatari.

"Sun yi awon gaba da wani Alhaji Ali Dankoli mai shekaru 70 da wata Zainab Isah mai shekaru 25.

"A saboda hakan, 'yan sanda sun yi gaggawar hanzartawa tare da rufe dukkan hanyoyin shige da fice a kauyen sannan suka bibiyi miyagun.

"A wannan halin ne 'yan bindigan suka budewa 'yan sanda wuta, lamarin da ya kawo mutuwar dan sanda daya," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Da duminsa: Ana tsaka da korona, babban basarake Olu na Warri ya rasu

A wani labari na daban, Boss Mustpha, sakataren gwamnatin tarayya ya ce 'ya'yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, jaridar The Cable ta wallafa.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel