Da duminsa: Ana tsaka da korona, babban basarake Olu na Warri ya rasu

Da duminsa: Ana tsaka da korona, babban basarake Olu na Warri ya rasu

- Cike da alhin tare da koke-koke fadar Olu na Warri take a halin yanzu

- Hakan ya faru ne sakamakon rasuwar babban basaraken a yammacin ranar Litinin

- Zukatan iyalansa, dogarai tare da hakiman fadar ta fada cikin alhini tare da makoki

Jama'ar garin Warri ta jihar Delta sun wayi gari da wani labari mai firgita zukata.

Labari ne na rasuwar babban basaraken garin kuma shugabansu, Ogiame Ikenwoli.

Ya rasu a ranar Litinin, 21 ga watan Disamban 2020 da yammaci. Hakan ya kawo sanadiyyar harsgitsewar gidan sarautar da koke-koke tare da makoki.

Ba 'yan gidan sarautar wannan rasuwar ta girgiza ba, hatta hakimansa da dogaransa sunyi matukar jin rasuwarsa.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba zan goyi bayan tsige shugaban kasa Buhari ba, Lamido

Duk da har a yanzu ba a samu wani cikakken bayani daga fadarsa a kan musababin mutuwarsa ba, jaridar The Nation ta ruwaito cewa rashin lafiyar basaraken yayi kamari a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamban 2020.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel