Kwayar cutar B.1.1.7 lineage ta bayyana a Osun inji Shugaban cibiyar ACEGID
- Masana sun ce an fara samun masu dauke da kwayar SARS-CoV-2 a Najeriya
- Africa Centre of Excellence for Genomics of Infectious Diseases ta gano wannan
- Shugaban cibiyar binciken yace N501Y, A570D da HV 69 – 70 ba su bayyana ba
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa sabuwar nau’in Coronavirus da yanzu haka ya ke tada hankalin al’umma ya bayyana a Najeriya.
Kwararrun masanan da ke aiki da cibiyar bincike kan cututtuka masu yaduwa a Afrika ta jami’ar Redeemers-Ede, Osun, su ka tabbatar da wannan.
Ana yi wa sabon nau’in COVID-19 wanda aka gano a Ingila a watan Satumba lakabi da lineage B.1.1.7.
A wani rubutu da masanan da ke aiki da wannan cibiya ta ACEGID su ka fitar a shafin Virological, sun yi ikirarin ganin cutar a jikin mutane a Osun.
KU KARANTA: Tambayoyi da amsa game da maganin COVID-19
Masanan sun ce sun fara ganin cutar ne a jihar Osun a jikin wani da aka dauki jininsa a Agusta. A watan Oktoba, aka sake ganin da cutar a jikin wani.
A dalilin barkewar cutar ne kasashen Duniya da-dama su ka sa takunkumin hana shiga Ingila, sannnan su ka hana mutanen yankin zuwa kasarsu.
Shugaban cibiyar bincike ta ACEGID, Farfesa Christian Happi wanda ya kware sosai a kan wannan harka ya ce sun ga B.1.1.7 lineage a Najeriya.
Duk da karuwar cutar COVID-19 da ake samu, Farfesan ya ce kawo yanzu 1% na masu jinya a Najeriya ne su ka kamu ta kwayar cutar SARS-CoV-2.
KU KARANTA: Uwargidar Najeriya Aisha Buhari ta tafi Dubai neman magani
Masanin ya kuma bayyana cewa sauran nau’ukan COVID-19 irinsu N501Y, A570D, da HV 69 – 70, ba su kai ga bayyana a jikin mutanen kasar ba tukun.
Tun a jiya ku ka ji cewa sabuwar kwayar COVID-19 ta fara tsorata gwamnatin Najeriya, har an kai ga tunanin lafta takunkumi domin dakile yaduwar cutar.
Barkowar samfurin Coronavirus na SARS-CoV-2 ya sa kasashe sun daina zirga-zirga zuwa Ingila, inda irin wannan kwayar cuta ya fara bayyana kwanaki.
Gwamnatin Tarayya ta ce COVID-19 da ta dawo ta na da ban tsoro, dole a firgita da irin hadarinta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng