Muhimman tambayoyi 6 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona

Muhimman tambayoyi 6 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona

- A ƙarshe, an samar da ingantaccen maganin riga-kafin cutar COVID-19 a ƙasar Amurka, Burtaniya da wasu manyan ƙasashe da ke faɗin duniya.

- Alamu sun tabbatar da samun sauki daga wannan magani duk da cewa cutar na neman sake dawowa a karo na biyu.

- Sai dai duk da haka, riga-kafin na iya kare mutum daga sake kamuwa da cutar duk da akwai alamun tambayoyi kan hakan

Shafin Legit.ng ya samo muku wasu ingantattun bayanai da ya kamata kowanne ɗan Najeriya ya sani dangane da wannan magani na riga-kafi, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

1. Me ake nufi da riga-kafi?

Riga-kafi ana samar da shi ga kwayoyin cutar 'virus' mai rai da ko kuma mataccen kwayar virus din da ya taba shafar mutum domin daidaituwar jikin dan Adam da kuma samar da garkuwa daga sake kamuwa daga wannan kwayar cuta.

2. Me ya sa riga-kafi ke da mahimmanci?

Yayin da cutar ta shiga jikin ɗan Adam, nan take garkuwar jiki za ta fahimci cutar ta fi karfin ta, ta hanata tasiri.

3. Tsawon wanne lokaci garkuwar ke aiki jikin mutum?

Bayanai na gwajin likitoci sun nuna cewa maganin riga-kafin kamfanin Pfizer, wanda ingancinsa ya kai kashi 95. Aikin maganin na kai tsawon wata biyu, yayin da shan maganin a karo na biyu na bayar da cikakkiyar kariyar da ake buƙata.

KARANTA: Mu da su za'a ga waye zai gaza: Sha'aban Saharada ya ja layi tsakaninsa da Ganduje

Muhimman tambayoyi 6 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona
Muhimman tambayoyi 6 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona
Asali: UGC

4. To wa ya cancanci a yiwa maganin riga-kafin?

Kowanne mutum ya kamata a yi masa domin yaƙi da cutar baki daya amma mutanen da ake ganin sun fi hatsarin kamuwa da ita, su ya fi cancanta da a yi musu tukunna.

KARANTA: AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce

5. Shin riga-kafin bai da wata illa?

Bayanan gwajin likitoci ya nuna cewa tabbas rikafin yana da wasu illoli kamar: zafin allura, zazzaɓi, gajiya, ciwon kai, ciwon jiki da na gabobi. Amma wannan na ɗan wani lokaci ne kadan kafin su wuce.

6. Shin zai iya hana yaɗuwar kwayar cutar COVID-19?

Tun da fati dai an samar da maganin ne domin hana kamuwa da rashin lafiya amma babu tabbacin zai hana yaɗuwar kwayar cutar ta COVID-19. Shi ya sa yake da matuƙar mahimmanci ɗaukar matakan kariya daga kamuwa da cutar.

7. Nawa ne tsadarsa?

Masu samar da magungunan ke da alhakin iyakance kuɗin da za su caji amma ya danganta da yadda aka samar da shi ga tsarin kamfanoni lafiyar inshora na gwamnati da kuma masu zaman kansu ko kuma tallafin gwamnati akan samar da shi.

A makon jiya ne Legit.ng ta rawaito cewa rundunar soji ta fitar da sanarwar cewa annobar Korona ta hallaka Janar Olubunmi Irefin sakamakon kamuwa da kwayar cutar.

Sai dai, ma su fada a ji daga yankin da marigayin ya fito sun ce sam basu gamsu cewa zai kamu da korona har ta hallaka shi duk cikin kwana uku kacal ba.

Mutanen sun yi zargin cewa an gaggauta binne gawar marigayi Janar Irefin ba tare da barin makusantansa sun shirya gawarsa ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng