Gwamnatin Tarayya ta na lissafin haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje

Gwamnatin Tarayya ta na lissafin haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje

- Minista, Lai Mohammed yace sabuwar COVID-19 da ta bullo tana da hadari

- Kwayar cutar ta sa an fara barazanar haramta zuwa wasu kasashen ketare

- Babu mamaki PTF ta ba Gwamnatin shawarar a dauki wannan mataki yau

Barkowar sabuwar samfurin kwayar cutar COVID-19 a Ingila ya sa gwamnatin tarayya ta na tunanin haramta tafiya zuwa wasu kasashen Duniya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya na cewa gwamnatin tarayya ta na iya garkama wani takunkumin.

Idan aka sa takunkumi, za a hana zuwa wasu yankuna a Duniya,sannan za a haramtawa mutanen da suka fito daga wuraren nan su shigo Najeriya.

Kamar yadda hukumar dillacin labarai na kasa ta bayyana, Ministan ya yi wannan magana ne dazu.

KU KARANTA: Najeriya ta kawo wata dabarar fasaha domin rage fasa-kauri

Lai Mohammed wanda yana cikin kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar COVID-19, ya ce gwamnati ta san da zaman barnar da cutar ta dawo yi.

Ministan tarayyan ya ce ba za su yi watsi da yiwuwar sake hana fita da shigowa Najeriya ba.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto shi ya na cewa: “Mun fi damuwa da sabuwar irin COVID-19 wanda ta ke bayyana a Birtaniya; samfurin da ya hayayyafa.”

Lai Mohammed ya bayyana ta’adin cutar, ya ce: “Tana da wahalar a gano ta, tana yaduwa sosai, kuma mutane suna mutuwa bayan kankanin lokaci da gano cutar.”

KU KARRANTA: An shiga kotu kotu da Atiku, ana zarginsa da kin biyan bashi

Gwamnatin Tarayya ta na lissafin haramta tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje
Alhaji Lai Mohammed Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

“Wannan abu damuwa ne gare mu a matsayinmu na kasa.”

Ministan yace babu mamaki a taron yau a bada shawarar a hana zuwa wasu kasashe. A irin wannan lokaci ne ‘yan Najeriya da ke Ingila suke dawowa.

Kwanakin baya, Atiku Abubakar ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta hana duk wani jirgi zuwa kasar Ingila, sannan ta hana jiragen can shigowa Najeriya.

Atiku Abubakar ya gargadi gwamnati ta hana zirga-zirgan jirage tsakanin Najeriya da Ingila.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce hakan ya zama dole ne domin dakile yaduwar sabon nau'in annobar COVID-19 ta da bulla a Landan kwanan nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel