Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha kan kazafi

Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha kan kazafi

- Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta damki Alibaba, mai baiwa gwamnan Kano shawarwari a kan harkar addini

- Ta zargi Alibaba da jingina wa Kwankwaso mallakar Kamfanin Dangote Oil a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo

- Da kyar aka bayar da belinsa bisa sharadin komawa gidan rediyon ya karyata kansa da kansa, kuma sai da yayi hakan

Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta damki Ali Muhammad Alibaba, mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara na musamman a kan harkokin addini, bisa ikirarin da yayi a kan Rabiu Kwankwaso.

Ali Baba ya ce Aliko Oil Company Limited mallakin Kwankwaso ne a wata hira da aka yi dashi a wani gidan radiyo.

A tattaunawar, Alibaba ya bukaci Kwankwaso ya fito fili yayi rantsuwa a kan cewa ba kamfaninshi bane. A cewar Alibaba, kalar kamfanin ja da fari ne, kuma hakan yayi kama da kalar da kwankwaso yake amfani da ita a siyasarsa.

Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha a kan karya
Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha a kan karya. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

Ma'aikatan Aliko Oil sun hassala da wannan magana tashi, sai suka kai karar Alibaba hedkwatar 'yan sanda ta Kano da ke Bompai.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai a kan yadda 'yan sanda suka gayyaci Alibaba don ya amsa tambayoyinsu, sai kuma suka rike shi.

Bayan kwashe sa'o'i suna tambayarsa, sai suka bayar da belinsa, da sharadin zai koma har gidan rediyon da yayi maganganun ya karyata kansa.

A ranar Asabar, Alibaba ya bayyana a shirin gidan rediyon, ya baiwa kamfanin hakuri bisa alakantasu da tsohon gwamnan da yayi.

KU KARANTA: Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

Da aka tambayi kakakin 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, cewa yayi ba shi da labari a kan faruwar lamarin, saboda yayi tafiyar 'yan kwanaki.

A wani labari na daban, cike da farin ciki tare da mika godiya ga Ubangiji, iyayen daliban makarantar gwamnati ta Kankara da aka sace a ranar Juma'a sun taru a farfajiyar makarantar.

Hakan ta faru ne bayan da aka cteo daliban da 'yan bindiga suka sace a ranar Juma'a da ta gabata a garin Kankara.

Bayan samun ceto daliban, an garzaya da su gidan gwamnatin jihar Katsina da safiyar yau Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel