Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu

Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu

- Malam Garba Shehu ya bukaci wadanda suka kalmashe kudaden gangamin BringBackOurBoys da su mayar wa wadanda suka dauka nauyinsu

- Hadimin shugaban kasan ya ce tuni wasu marasa kishin kasa suka shirya tsaf domin yin gangami amma sai ga shi an ceto yaran

- Ya ce ceton yaran abu ne da duk wani mai tausayi a fadin duniya zai yi murna amma marasa kishin kasa ba za su yi ba

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan harkar yada labarai, Garba Shehu, ya yi kira ga masu gangamin BringBackOurBoys da su mayar da kudaden da suka karba domin gangamin.

Ya jajanta lamarin tare da cewa babban abun kunya ne garesu da za su yi amfani da satar yaran makaranta da aka yi a Kankara jihar Katsina su tada hankula.

Shehu ya ce wadanda suka kirkiri BringBackOurBoys ba su da kishin kasa, ThePunch ta wallafa.

An fara gangami kala-kala a kafafen sada zumuntar zamani bayan sace yaran makaranta da 'yan bindiga suka yi a ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020 a Katsina.

Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu
Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Hotunan 'yan makarantar Kankara suna isa gidan gwamnatin Katsina

'Yan bindiga a kan babura sun kai hari makarantar inda suka yi awon gaba da dalibai masu tarin yawa bayan sa'o'i kadan da isar shugaban kasa Muhammadu Buhari garin Daura.

Gwamnan jihar Katsina ya sanar da cewa an sako yaran 344 bayan kwanaki kadan da 'yan bindiga suka iza keyarsu daga makaranta.

A yayin da wasu 'yan Najeriya ballanta iyayen yaran ke cike da farin ciki, wasu kuwa basu ji dadin hakan ba.

Garba Shehu a ranar Lahadi ya ce a kowanne sashi na duniya dole a ji dadin samo yaran da aka yi amma fa idan akwai tausayi ba lamarin siyasa ba aka saka gaba.

KU KARANTA: Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

A wani labari na daban, daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da 'yan bindiga suka sace sun iso gidan gwamnati.

Jami'an tsaro ne suka yi musu iso har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina.

A ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel