'Yar aljanna: Matar aure ta kwarara wa mijinta addu'o'i bayan ya yi wuf da dalleliyar amarya

'Yar aljanna: Matar aure ta kwarara wa mijinta addu'o'i bayan ya yi wuf da dalleliyar amarya

- Maimakon ta daga hankalinta, wata mata ta wallafa irin farin cikin da take yi bayan mijinta yayi mata kishiya

- A cewar Safa, mazauniyar New Jersey, ta fi mijinta farin ciki kuma tana so a taya ta da addu'a da fatan alkhairi

- Ta wallafa hakan ne a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter cike da annashuwa

Wata musulma ta bayyana farin cikinta bayan mijinta ya dankara mata kishiya. Safa, wacce mazauniyar New Jersey ce, ta wallafa hakan a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 19 ga watan Disamba, inda tayi wa iyalinta fatan tsarin Allah.

"Allah ka tsaremu daga 'yan hassada da miyagun idanu", ta wallafa hakan ne yayin da take murna a kan mijinta ya kara aure.

"Jama'a an yi min kishiya!!!!! Na fi mijina farin ciki, Allah ya kara mana dacewa kuma ya karemu daga 'yan hassada da migayen idanu. Ameeen" kamar yadda ta wallafa.

KU KARANTA: Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

'Yar aljanna: Matar aure ta kwarara wa mijinta addu'o'i bayan ya yi wuf da dalleliyar amarya
'Yar aljanna: Matar aure ta kwarara wa mijinta addu'o'i bayan ya yi wuf da dalleliyar amarya. Hoto daga @Bellahijabi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yajin aiki: Abinda aka tattauna tsakanin ASUU da FG a dogon zamansu

Mutane da dama sun yi ta yaba mata bisa amincewar da tayi da kishiyarta.

Sai dai wallafar ta janyo mata caccakar wasu 'yan Najeriya. Wata Vivian Akinosoye cewa tayi, rayuwar yaranta ba za ta taba zama iri daya ba, bayan mijinta ya kara aure.

Anan Safa ta mayar mata da martani, inda tace "Yaranmu suna nan lafiya lau. Duk abinda Ubangiji ya so ya faru, babu makawa zai faru. Ubangiji yayi miki jagora. Ameen.

"Duk mutumin da yace kara aure laifi ne a Amurka, ya tafi wuta cikin salama."

Ta kara da cewa, "Duk abinda mace za ta so wa kanta, ya kamata ta so ma 'yar uwarta, matsawar mace ta hada kai da 'yar uwarta kuma ta yarda da Allah Subhanahu wa ta a'la,"

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng