Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

- Hadimin shugaba Buhari na harkar labarai ya ce akwai wadanda suke alhinin sako daliban GSSS Kankara

- A cewar Bashir Ahmad, dama tun satar daliban, akwai wadanda suka shiga farin ciki, murna har da shagulgula

- Ahmad ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan sakin yaran

Hadimin shugaba Buhari na musamman a kan harkokin labarai, Bashir Ahmad, ya ce wasu sun yi takaicin yadda aka sako daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina.

"Bayan an sace daliban, alamu sun nuna karara cewa akwai wadanda suka yi farin ciki kwarai. Kuma bayan an sako yaran, akwai wadanda suka shiga alhini. Najeriya za ta cigaba da samun nasara," kamar yadda Ahmad ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a ranar Alhamis ya tabbatar da sakin yaran guda 344, ya kara da cewa yaran suna Tsafe, jihar Zamfara, kuma za a kama hanyar Kankara da su ranar Juma'a. A cewarsa, ba a biya 'yan ta'addan ko sisi ba, kafin su sako daliban.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a

Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari
Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da ambasadan Najeriya a kasar Chadi, Zannah Umar Bukar Kolo, sun hadu da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby da ambsadan kasar Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimi, a ranar Laraba don tattaunawa a kan hanyoyin mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya da ke kasar.

KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Zahra Buhari tayi ga mijinta a cikarsu shekaru 4 da aure

Da yawa daga cikin 'yan gudun hijiran, sun tsere ne daga jihar Borno zuwa Chadi tun 2014, sakamakon hare-haren Boko Haram.

Mai baiwa gwamna Zulum shawara na musamman a kan harkar labarai, Malam Isa Gusau, yace sun yi taron ne don bin hanyar da za a mayar da 'yan gudun hijirar zuwa Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel