'Yan sanda sun kama wasu da suka yi yunƙurin fashi da bindigar roba a Legas

'Yan sanda sun kama wasu da suka yi yunƙurin fashi da bindigar roba a Legas

- Ƴan sanda sun yi nasarar dakile fashi da aka so yi a gadar Otedola da ke Legas a babban titin Lagos zuwa Ibadan

- Yan sandan sun kuma yi nasarar damƙe mutum biyu da ake zargi inda aka same su da bindigar roba da muggan makamai

- Kwamishinan yan sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu ya bada umurnin fara bincike a kansu kafin gurfanar da su a kotu

Jami'an yan sandan rundunar masu amsa kira cikin gaggawa, RRS, sun daƙile wani yunkurin fashi da makami da aka yi a yayin cinkoson motoci a Legas.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, kakakin yan sandan jihar, Olumuyiwa Adejobi ya ce an kama wadanda ake zargin su biyu, The Punch ta ruwaito.

'Yan sanda sun ɗaƙile fashi a gadar Otedola, sun kama waɗanda ake zargi
'Yan sanda sun ɗaƙile fashi a gadar Otedola, sun kama waɗanda ake zargi. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

Adejobi ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a gadar Otedola da ke kan babban titin Lagos zuwa Ibadan.

DUBA WANNAN: Aisha Gombi: Zulum ya naɗa jarumar mafarauciyar da Boko Haram ke 'tsoro' muƙami a gwamnatinsa

Ya ce ana zargin mutanen biyun da aka kama yan kungiyar asirin Awawa ne da ke Oko-koto, Agege.

A cewarsa, ƴan sandan ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar, Yinka Egbeyemi, a ranar Juma'a sun haɗu da waɗanda ake zargin yan fashin ne a gadar Otedola misalin ƙarfe 11 na dare a gadar Otedola.

"Cikin gaggawa yan fashin suka yi fatali da babur dinsu mai lamba NND 268 WZ da bindigan roba da wasu miyagun makamai," in ji jami'in ɗan sandan.

KU KARANTA: Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria

Ajejobi ya ce daga bisani an damƙo wadanda ake zargin a maɓuyarsu da ke Agege kamar yadda kwamishinan yan sandan Legas, Hakeem Odumosu ya bada umurni.

Kakakin yan sandan ya ce Odumosu ya bada umurnin a fara bincike kansu nan take daga bisani a gurfanar da su gaban kotu.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel