Aisha Gombi: Zulum ya naɗa jarumar mafarauciyar da Boko Haram ke 'tsoro' muƙami a gwamnatinsa

Aisha Gombi: Zulum ya naɗa jarumar mafarauciyar da Boko Haram ke 'tsoro' muƙami a gwamnatinsa

- Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya naɗa, mafarauciya, A'isha Gombi mai bashi shawara

- Zulum ya naɗa ta mai bada shawara kan yaƙi da ta'addanci ne don gudunmawa da jarumtar ta a yaƙi da ta'addanci

- Zulum ya bukaci ta zage damtse ta kuma cigaba da aikin tuƙuru kamar yadda aka santa don cimma manufofin gwamnatin

Gwamnan Jihar Borno, Umara Zulum, ya nada mashahuriyar yar farauta haifaffiyar jihar Adamawa, Aisha Gombi, a matsayin mai bada shawara a yakin da ake da Boko Haram, Premium Times ta ruwaito.

Kungiyoyin fararen hula, ciki har da mafarauta, suna taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da ta'addancin da ya dauki tsawon shekaru goma a arewa maso gabas.

Boko Haram: Zulum ya naɗa jarumar mafarauciya matsayin mai bada shawara
Boko Haram: Zulum ya naɗa jarumar mafarauciya matsayin mai bada shawara. Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

Mafarauciyar, "sarauniyar maharba" ta daɗe tana taimakawa jami'an tsaro wajen yaƙi da Boko Haram, yan bindiga da kuma sauran ayyukan ta'addanci a arewa maso gabas, a cewar gwamnan.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace basaraken jihar Kogi yana dab da shiga masallaci

A wata sanarwa da Danjuma Ali, babban sakatare, kuma shugaban ma'aikatan sakataren gwamnan jihar ya ce nadin ya fara aiki tun 7 ga watan Disamba.

Sanarwar ta ce muƙamin ya na da nasaba da "bibiyan ayyukan Aisha Gombi da ka yi" kuma an bukaci da ta sake tsage damtse.

"Naɗin ya fara aiki tun 7 ga Disamba," a cewar sa.

KU KARANTA: An yi wa mutane 8 da suka rasu a tawagar Sarkin Kauran Namoda sallah (Bidiyo)

Ya kuma yi bayanin takardar naɗin a takaice.

"Ina mai farin cikin sanar da ke cewa mai girma gwamna, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da naɗin ki a matsayin mataimakiya ta musamman gareshi.

"An naɗa ki saboda ƙwazonki da fasaharki, sanin aiki da kuma taimakawa al'umma.

Ana tsammanin cewa zaki kare mutuncin kujerar ki, ki kuma nuna ƙwazon da aka sanki dashi ta hanyar yin aikin ki yadda ya dace don cimma munufofin gwamnati," kamar yadda ya ke a rubuce cikin takardar naɗin.

A wani rahoto da Legit.ng ta taba wallafawa na hirar da aka yi da Aisha Gombi, ta ce 'yan Boko Haram sun san kuma suka shakkar ta.

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel