'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya

'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya

Mace guda daya tilo, Aisha Bakari Gombi, cikin mafarautan dake aiki da dakarun soji a jihar Borno ta bayyana cewar ba zata samu kwanciyar hankali ba sai ta kubutar da 'yan Chibok daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

A wani faifan bidiyo da kafar yada labarai ta Al-Jazeera a kan rayuwar ta, Aisha, ta bayyana cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun santa kuma suna tsoron ta.

Cikin faifan bidiyon, mijin Aisha ya bayyana cewar da goyon bayansa take fita farautar 'yan Boko Haram har dajin Sambisa.

'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya
Aisha mafarauciya

Jarumta da bajintar da Aisha ke nunawa ya saka mahaifinta mallaka mata bindigar sa da yake fita farauta da ita.

DUBA WANNAN: Fallasa: An tafka magudi a zaben 2015 a arewa - Dattijo Tanko Yakasai

Da take bayyana irin kalubalen da take fuskanta, Aisha, ta ce babban burinta shine ta kama ko hallaka wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ake kira Bula Yaga wanda ta ce ya kware wajen keta musamman ga mata da kananan yara.

'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya
Aisha mafarauciya da Mijinta

Aisha ta shaidawa Al-Jazeera cewar sau biyu tana yin gaba-da-gaba da Bula Yaga amma bata samu nasarar kashe shi ko kama shi ba.

Ta kara da cewar, Bula Yaga, ne keda iko da wani yanki na dajin Sambisa da har yanzu babu wanda ya isa ya je wurin saboda tsoron shu'umancin sa.

'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya
Aisha mafarauciya yayin fita Farauta

Aisha ta bayyanawa Al-Jazeera cewar ta gaji farauta ne wurin mahaifinta kamar yadda shima ya gada wurin mahaifinsa.

Aisha ta bayyana cewar ta fuskanci kalubale bayan ta kasa samu ciki bayan aurenta, dalilin da ya saka aurenta na farko mutuwa. Saidai yanzu haka Aisha na dauke da juna biyu kuma hakan yanzu ya saka ta rage fita domin kulawa da juna biyun da take dauke da shi.

'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na - Aisha mafarauciya
Aisha da ragowar mafarata Maza

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel