AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce

AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce

- Har yanzu batun sace daliban Kankara bai kare ba duk da ceto yaran da aka yi garkuwa da su

- Akwai ma su ra'ayin cewa an kitsa sace daliban tare da kubutar da su domin cimma wata manufa

- Kungiyar 'yan kabilar Yoruba, Afenifere, ta ce batun sace dalin da kubuat da su duk shiri ne, tsara shi aka yi

A wani jawabi da ta fitar ta hannun sakatarenta, Yinka Odumakin, kungiyar inganta zamantakewa da bunkasa siyasayar 'yan kabilar Yoruba (Afenifere) ta yi martani a kan sace daliban Kankara da sakinsu.

Kungiyar, a cikin martaninta, ta bayyana sace daliban da kubutar da su a matsayin babbar damfara da shirin wasan kwaikwayo, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Jawabin ya bayyana cewa: "duk masu tunanin cewa akwai sauran wani abu da ya rage a cikin wannan kasa mai ban dariya da ake kira Nigeria ya kamata su sauya tunani, idanuwansu su bude bayan wasan da aka shirya na sace daruruwan dalibai a Kankara.

KARANTA: Kar kan ku ya kulle: Buharin ne shugaban ƙasa ba Jubril Sudan ba; Femi Adesina ya yi raddi

"An so yin kwatankwacin irin wannan wasan da 'yammatan makarantar Chibok da aka sace a shekarar 2014, banbancin kawai na gwamnati ne, sannan kuma an samu salwantar rayuka a wancan.

AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce
AFENIFERE: Satar daliban Kankara da kubutar da su duk damfara ce @Bashir Ahmad
Source: Facebook

"An sake maimaita irin abinda ya faru a Chibok a yayin da aka sace daruruwan dalibai bayan shugaba Buhari ya isa Katsina. An sace yaran da tsakar rana a hanyoyin da sojoji ke sintiri kamar a Chibok.

KARANTA: Siyasar Kano: An yi hannun riga tsakanin Ganduje da Sha'aban Sharada

"Mu, a Afenifere, mu na jin haushin ake kiranmu 'yan Nigeria saboda rashin daukar rayuwa da muhimmanci da shugabanninmu ke yi.

MUn tabbata an yi amfani da rayuwar wadannan kananan yara domin wata manufa kuma dole kudi ya kara shiga hannun 'yan ta'adda da ke hana kasa da jama'a zaman lafiya.

"Mu na kira ga wayayyun 'yan arewa su tashi domin neman kawo karshen wannan rashin hankali, bai kamata mu bari ake irin wannan wasa a shugabancinmu ba.

"Lokaci ya yi da ya kamata mu kubutar da Nigeria, mu tashi, mu fi karfin kananan banbance."

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020, gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa an saki daliban GSSS Kankara da aka sace.

A cewar gwamnan, shugabannin kungiyar makiyaya na MACABAN/Miyetti Allah su ka shiga, su ka fita wajen ganin wadannan yara sun kubuta.

Mai taimakawa Mai girma gwamnan a kan sha’aninn tsaro, Mallam Ibrahim Katsina, ya tabbatar da hakan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel