Kwankwaso ya kaddamar da sansanin Alhazai a Edo
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da sansanin Alhazai a jihar Edo
- Kwankwaso ya kuma yi wa Gwamna Godwin Obaseki, dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar mai zuwa kamfen
- Ya bukaci al'umman Musulmi musamman wadanda suka fito daga yankin arewacin kasar da su duba girmansa su sake zabar Obaseki da mataimakinsa
Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki da tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, sun kaddamar da sansanin Alhazai a Benin, babbar birnin jihar Edo.
Sun kuma bukaci al’umman Musulmi a jihar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar 19 ga watan Satumba domin tabbatar da sake zabar Gwamna Obaseki wanda yake dan takarar PDP da mataimakinsa, Rt. Hon. Comr. Philip Shaibu.
Kwankwaso ya jinjinawa kokarin gwamnan a fadin jihar, inda ya ce nasarorin da Obaseki ya samu a mulkinsa na farko zai sa a sake zabarsa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki
Tsohon gwamnan ya ce: “Bari kuma na gode ma mutanen Edo da Musulmai a jihar a kan tarin goyon bayan da suka bayar wajen cimma nasarar da ke kasa ta bangaren ci gaba.
“Wannan ne lokacin da dukkaninmu masu katin zabe kuma wadanda muka cike ka’idar yin zabe za mu fito kwanmu da kwarkwatarmu domin tabbatar da mun zabi jam’iyyar PDP.
“Ina kuma rokon ku dukka musamman wadanda suka fito daga yankin arewacin kasar da ku tabbatar kun zabi jam’iyyar PDP a zaben ranar 19 ga watan Satumba, 2020.
“Dan Allah ku zabi PDP, ku kare kuri’unku sannan ku tabbatar da Obaseki da mataimakinsa, Shaibu sun yi nasara a zaben jihar mai zuwa ina kuma kira a kan ku tabbatar da kun yi addu’a na zaman lafiya a jihar.
“A ranar zabe ku tuna abunda gwamnan ya yi wa Musulmi da al’umman jihar Edo gaba daya. Ina farin ciki da samun damar kaddamar da wannan sansani na Alhazai. Nagode ya mai girma a kan yadda ka tafiyar da Musulmai da kuma goyon bayan da ka basu a jihar,” in ji Kwankwaso.
A nashi bangaren, Obaseki ya yi wa Musulmi godiya a kan tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da sauran addinai a jihar.
Ya ce zaman lafiyar da ala samu a jihar ya sa an samu ci gaba a dukkanin kananan hukumomi 18.
KU KARANTA KUMA: Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa
Gwamnan ya kuma yaba ma tsohon Gwamna Kwankwaso a kan haduwa da yayi dashi wajen kaddamar da sansanin Alhazan, inda ya ba al’umman Musulmi tabbaci samun karin ayyukan ci gaba idan aka sake zabarsa.
A gefe guda, sifeton janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya tura wasu manyan jami'an 'yan sanda zuwa jihar Edo domin su saka ido a kan zaben kujerar gwamna mai zuwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng