Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada

Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada

- Bangaren jam'iyyar PDP a Kano masu yi wa Wali biyayya ta kori Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar

- Hakan na zuwa ne bayan wani taro da bangaren ta yi a ranar Alhami inda ta ce ta kore shi ne bisa zargin yi wa jam'iyya zagon kasa

- Har wa yau, bangaren na Wali ta yi ikirarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya karya wasu dokokin kudin tsarin jam'iyyar

Wani abu mai kama da drama ya faru a ranar Alhamis a yayin da bangaren jam'iyyar PDP ta Jihar Kano masu yi wa tsohon ministan harkokin kasashen waje, Aminu Wali, biyaya ta kori tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga jam'iyyar kan zarginsa da aikata ayyukan zagon kasa ga jam'iyya.

Bangaren na Wali ta zargi tsohon ministan tsaron kuma mai neman takarar shugabancin kasa a karskashin PDP a 2019 wato Kwankwaso da 'karya dokokin da ke kundin tsarin jam'iyyar ta PDP, The Nation ta ruwaito.

Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada
Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

Bangaren da Wali ke yi wa jagora ta sanar da korar Kwankwaso daga jam'iyyar jim kadan bayan ta zabi sabbin shugabanni a jam'iyyar da zasu jagoranci sabuwar bangaren.

An dade ana samun rashin jituwa tsakanin bangaren Wali da masu tafiyar Kwankwasiya a jam'iyyar ta PDP.

A baya bayan nan kotu ta zartar da hukuncin cewa kwamitin wucin gadi da Kwankwaso ya kafa itace halastacciyar shugabancin jam'iyyar.

Wannan hukuncin kotun ya saka 'yan Kwankwasiyya zaben sabbin shugabannin jam'iyya a ranar Litinin.

An zabi Shehu Sagagi a matsayin shugaba; Danraka Hussaini Bebeji ya zama mataimakin shugaba yayinda Jamilu Abubakar Danbatta ya zama sakataren jam'iyya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura

Amma bangaren Aminu Wali ba su gamsu da wannan hukuncin da kotu ta yi ba don haka suka garzaya kotun daukaka kara don kallubalanta hukuncin da karamar kotun ta yanke.

Baya ga korar Kwankwaso, bangaren na Wali ta zabi sabbin shugbannin jam'iyya 39 da za su cigaba da jan ragamar harkokin jam'iyyar.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164