Boko Haram: Zulum ya gana da shugaba Deby a kan 'yan gudun hijiran Borno a Chadi
- Gwamnan Babagana Zulum na jihar Borno da ambasadan Najeriya a Chadi, sun kai ziyara kasar Chadi
- Sun je don ya mika sakon godiya ga shugaban kasar Chadi bisa karamcin da ya nunawa 'yan Najeriya
- Ya kuma nemi su tattauna a kan hanyar mayar da 'yan gudun hijirar Borno da ke Chadi zuwa Najeriya
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da ambasadan Najeriya a kasar Chadi, Zannah Umar Bukar Kolo, sun hadu da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby da ambsadan kasar Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimi, a ranar Laraba don tattaunawa a kan hanyoyin mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya da ke kasar.
Da yawa daga cikin 'yan gudun hijiran, sun tsere ne daga jihar Borno zuwa Chadi tun 2014, sakamakon hare-haren Boko Haram.
Mai baiwa gwamna Zulum shawara na musamman a kan harkar labarai, Malam Isa Gusau, yace sun yi taron ne don bin hanyar da za a mayar da 'yan gudun hijirar zuwa Najeriya.
KU KARANTA: Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG
A taron, Gwamna Zulum yace, "Mutanen mu suna jin dadi, gwamnatin Chadi tana kulawa dasu. Na zo ne don in mika sakon godiyata ga shugaban kasa a kan karamcin da ake bai wa mutanenmu a nan Chadi.
"Muna so mu yi magana a kan yadda za mu mayar da mutanenmu Najeriya. Amma mun zo nan ne saboda abubuwa 3: Mu hadu da mutanenmu, mu yi godiya ga gwamnatin Chadi, sannan mu tattauna a kan yadda za mu mayar dasu wurare daban-daban a jihar Borno."
KU KARANTA: Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga
Gwamna Zulum ya ziyarci Chadi a watan Janairu, inda ya hadu da kwamandan MJTF a kan rashin tsaro. Ya kuma kai ziyara kasar Nijar da Kamaru a lokuta daban-daban, kamar yadda SA din shi ya sanar a takarda.
A wani labari na daban, satar daruruwan daliban Kankara na jihar Katsina ya janyo alamomin tambaya a kan matsalar tsaro, wanda hakan ya rikita tunanin iyaye da dama, Daily Trust ta ce.
Daya daga cikin iyayen, Hajiya Marwa Hamza, wacce aka sace dan ta da jikanta a daren Juma'a, cikin GSSS Kankara, ta bayyana irin tashin hankalin da ta shiga.
A cewarta, "Ban taba shiga damuwa ba a rayuwata irin wannan. Na san yadda ake ji idan dan uwan mutum ya rasu, saboda na rasa mahaifina, kuma na san mutuwa dole ce, dole mutum yayi hakuri. Amma wannan ba kamar mutuwa bane, ba mu san halin da yaranmu suke ciki ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng