Kalamai masu ratsa zuciya da Zahra Buhari tayi ga mijinta a cikarsu shekaru 4 da aure
- Zahra Buhari, diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wallafa cikar aurenta shekaru 4 da mijinta
- Ta yi wallafar ne a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda ta bayyana soyayyarta ga mijinta
- A cewar Zahra, da Ahmed Indimi zai kara bukatar aurenta a karo na biyu, da ta kara amincewa
Zahra Buhari Indimi da mijinta Ahmed Indimi suna shagalin cikar aurensu shekaru 4 cur.
Zahra ta wallafa kalami masu nuna kaunarta ga mijinta, da fatan cigaba da rayuwa dashi a rayuwa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani na Instagram.
Kamar yadda Zahra ta wallafa: "Idan har akwai bukatar in kara aurenka, tabbas da na kara.
"Barka da zagayowar shekarun aurenmu 4, @ahmed.indimi, rayuwata ba za ta taba zama daidai ba idan da babu kai.
"Ya Allah, ka sanya ma'aurata su zama sanyin idanuwan juna. Ameen ya Wadud."
KU KARANTA: Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara
KU KARANTA: Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, a karkashin jam'iyyar APC, Daily Trust ta wallafa hakan.
Yarima, sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar tarayya, ya sanar da manema labarai kudirinsa a ranar Laraba a Abuja, inda yace yana son ya samu nasara don ya gyara rayuwar 'yan Najeriya ne.
Tsohon gwamnan ya bayyana tsananin takaicin da ya shiga bayan ganin yadda ake kashe-kashe a kasar nan duk da bakar fatara da talaucin da ke addabar 'yan Najeriya.
Yarima yace: "Idan ba a manta ba, a 2006, na bayyana kudirina na burin zama shugaban kasar Najeriya, bayan na mulki jihar Zamfara na shekaru 8."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng