BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'

BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'

- Mambobin CNG sun yi dirar mikiya a jihar Katsina, kuma yau ake sa ran za su fara zanga-zangar lumana

- Za su yi zanga-zargar zuwa Daura, inda shugaba Buhari yaje hutawa don su bayyana damuwarsu a kan masu garkuwa da mutane

- A cewar kungiyar, hare-hare ba za su hanasu isa wurin Buhari ba, don su yi korafi a kan kasa ceto daliban GSSS Kankara

Mambobin CNG sun yi wa jihar Katsina dirar mikiya don fara zanga-zanga ga hukuma a kan rashin ceto daruruwan daliban GSSS Kankara, jihar Katsina.

Sun sanya wa zanga-zangar #Bringbackourboys, wato a dawo mana da yara mazan mu, kuma za su fara zanga-zangar yau a jihar Katsina, Daily Trust ta wallafa.

Ana sa ran masu zanga-zangar za su nufi Daura don su bayyana damuwarsu ga shugaba Muhammadu Buhari, wanda har yanzu yana garin yana hutawarsa.

BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'
BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu bata gari suka lalata taron CNG na batun tsaro da aka yi a ranar Litinin, wanda aka yi a Kaduna.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ce hare-hare ba za su dakatar da su ba, kuma za su hadu da wasu don cigaba da kira don a sako yaran Kankara, cikin sauri, a raye kuma cikin koshin lafiya.

Suleiman ya ce CNG tana sane da yadda aka tattara jami'an 'yan sanda a jihar Katsina, kuma ya yi kira ga jami'an a kan kada su yi kokarin dakatar da halastacciyar zanga-zangar tasu, wacce za su yi ta cikin lumana.

KU KARANTA: Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa

"Ba zai yuwu a ce duk wani mai kishin arewa, kuma dan kasa nagari ya tankwashe hannayensa yana kallon masu garkuwa da mutane suna yin yadda suka ga dama a arewa ba. Wanda kowa ya san arewa wuri ne mai daraja a kasar nan."

A wani labari na daban, Sanata Rufai Hanga ya yi hasashen dalilin da yasa shugaba Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro.

Hanga ne sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar tarayya, ya sanar da Daily Sun dalilin da ya sanya Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro. Mutane da dama sun yi ta caccakar Buhari saboda kin sauke shugabannin tsaro.

Sanatan ya ce Buhari yana tsoron kananan jami'an tsaron da zai daura a kan mulki ba za su iya mara masa baya kamar wadannan shugabanni ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel