Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

- NGF ta ce tana da yakinin shugaba Muhammadu Buhari zai kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

- Kungiyar ta ce Shugaba Buhari mutum ne mai jajircewa da dagewa wurin shugabanci da kishin kasa

- Ta fadi hakan ne yayin taya shugaba Buhari, iyalansa da 'yan Najeriya murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC sun bayyana sakankancewarsu a kan shugaba Muhammadu Buhari, sun ce suna da tabbacin zai kawo karshen rashin tsaron da ke addabar Najeriya.

Sun bayyana hakan ne yayin taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Sun bayyana hakan a wata takarda mai taken: "Fatan alheri ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR a ranar zagayowar haihuwarsa ta 78," wacce shugaban PGF, Abubakar Bagudu ya sanya hannu a Abuja, a ranar Alhamis.

A cewarsa, PGF tana taya shugaba Buhari, iyalansa da kuma 'yan Najeriya murnar cikar shugaban kasa shekaru 78 da haihuwa, jaridar The Punch ta wallafa.

Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC
Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Zulum ya gana da shugaba Deby a kan 'yan gudun hijiran Borno a Chadi

Kamar yadda takardar tazo, "Mun yaba wa mulkinka da kuma dagewarka wurin ganin ka ciyar da Najeriya gaba. Duk da mawuyacin halin da kasar nan take ciki, muna da tabbacin cewa shugabancinka zai kawo karshen ta'addanci da rashin tsaron da Najeriya take fuskanta.

"Yayin da muke taya ka murnar zagayowar ranar haihuwarka, muna so muyi maka godiya sakamakon dagewarka da jajircewarka wurin shugabancin kasar nan. Muna matukar alfahari da shugabancin mutum mai kishin kasarsa irin ka."

KU KARANTA: BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'

A wani labari na daban, wani dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, Premium Times ta wallafa.

Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, ya bayyana canja shekarsa ta wata wasika wacce kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Alhamis.

Kamar yadda aka saba, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya bayyana rashin amincewarsa dangane da canja shekar Onuigbo, inda ya bukaci kakakin ya kwace kujerar, bukatar da bata samu karbuwa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel