Da duminsa: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC

Da duminsa: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC

- Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, Sam Onuigbo ya canja sheka

- Ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki, wato APC, kuma ya sanar da hakan a majalisa a ranar Alhamis

- Tun daga farkon wannan makon, 'yan majalisa 3 ne suka sauya sheka daga PDP zuwa APC, Onuigbo ne ya zama na hudu

Wani dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, Premium Times ta wallafa.

Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, ya bayyana canja shekarsa ta wata wasika wacce kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Alhamis.

Kamar yadda aka saba, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya bayyana rashin amincewarsa dangane da canja shekar Onuigbo, inda ya bukaci kakakin ya kwace kujerar, bukatar da bata samu karbuwa ba.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a

Da duminsa: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC
Da duminsa: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

KU KARANTA: Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa

Yanzu haka, 'yan majalisa 3 kenan suka canja sheka daga PDP zuwa APC daga farkon wannan makon. Onuigbo shine ya zama na hudunsu.

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, a karkashin jam'iyyar APC, Daily Trust ta wallafa hakan.

Yarima, sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar tarayya, ya sanar da manema labarai kudirinsa a ranar Laraba a Abuja, inda yace yana son ya samu nasara don ya gyara rayuwar 'yan Najeriya ne.

Tsohon gwamnan ya bayyana tsananin takaicin da ya shiga bayan ganin yadda ake kashe-kashe a kasar nan duk da bakar fatara da talaucin da ke addabar 'yan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel