Kaduna: El-Rufa'i ya bayar da umarnin rufe wuraren taron biki da gidajen rawar disko

Kaduna: El-Rufa'i ya bayar da umarnin rufe wuraren taron biki da gidajen rawar disko

- Ana cigaba da zaman dar-dar a Nigeria bisa fargabar sake dawowar annobar korona a karo na biyu

- Dalilan tsaro da kuma fargabar dawowar korona sun jawo rufe makarantu a wasu jihohin arewa

- Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki mataki na gaba bayan ta sanar da cewa a rufe wasu wuraren taron jama'a

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin rufe dukkan wasu wuraren taron biki, gidajen rawar disko, da cibiyoyin motsa jiki, a wani yunkuri na dakile yaduwar kwayar cutar korona a karo na biyu.

Kazalika, gwamnatin ta takaita harkokin wuraren sayar da abinci; babu zama a ci, sai dai a kunshewa mutum abincinsa ya tafi da shi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Bugu da kari, an umarci direbobi su rage yawan mutane da kaso 50 tare da tabbatar da cewa duk fasinjoji sun saka takunmi da kuma tabbatar da nesantar juna.

KARANTA: Majalisar wakilai: Honarabul Tajuddeen ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, ya bayyana dalili

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ne ya bayar da wannan umarni yayin wata hira da shi ta kai tsaye a yanar gizo da wasu gidajen radiyo da aka zaba.

Kaduna: El-Rufa'i ya bayar da umarnin rufe wuraren taron biki da gidajen rawar disko
Kaduna: El-Rufa'i ya bayar da umarnin rufe wuraren taron biki da gidajen rawar disko @Bashirahmad
Asali: Twitter

Ya bayar da umarnin ne bayan sauraron jawabin da kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Dakta Amina Baloni, ta gabatar.

Dakta Amina, a jawabinta, ta bayyana cewa ana samun mutane fiye da 100 da ke kamuwa da korona a jihar Kaduna a 'yan kwanakin baya bayan nan, lamarin da ya haddasa cikar cibiyoyin killacewa.

"An samu karuwar kaso 30 a kan adadin masu kamuwa da kwayar da cutar muke samu a baya, an samu hauhuawar alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar daga arewa da tsakiyar Kaduna.

"Akwai manya da yara daga cikin wadanda suka kamu da kwayar cutar, amma manyan mutane, yawancinsu ma'aikata, sune suka fi yawa," a cewarta.

Sai dai, El-Rufa'i ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ba yunkurin sake saka dokar kulle take yi ba.

Amma, ya yi kashedin cewa gwamnatin jihar Kaduna a shirye take ta dauki duk matakan da suka dace domin kare rayuka.

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Sanatoci sun koka akan gazawar shugaba Buhari wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fama da ita.

Sun kuma tunawa Shugaban ƙasar irin ƙarfin ikon da doka ta basu na tsige Shugaban ƙasa kamar yadda yake a kundin dokokin Najeriya.

Sanatoci sun yi niyyar ɗaukar ƙwararan matakai da suka haɗar da dakatar da kasafin kuɗin 2021, wanda hakan zai tilastawa shugaban ƙasa aiwatar da ƙudirinsu da gaske.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel