An taba dakatar da Adekolawole daga aiki a 1995 kafin zama Shugaban Poly, Ede

An taba dakatar da Adekolawole daga aiki a 1995 kafin zama Shugaban Poly, Ede

-An gano an taba samun John Adekolawole da laifin lalata da wata mata a 1995

-A dalilin haka aka dakatar da Dr. Adekolawole daga aiki, har aka hukunta shi

-Bayan shekaru 22 sai shugaban kasa ya nada shi Shugaban Federal Poly, Ede

Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa an taba kama shugaban makarantar Federal Polytechnic, Ede, da laifin lalata da wata mata a 1995.

Duk da danyen aikin da ya taba yi shekaru 22 da su ka wuce, Farfesa John Adekolawole, ya yi nasarar zama shugaban wannan babban makaranta ta koyon aiki.

An yi ram da John Adekolawole da laifin keta alfarmar wata Baiwar Allah a ofishinsa a lokacin ya na Darektan tsangayar kimiyya ta makarantar da ke jihar Osun.

Kamar yadda takardar da jaridar ta bankado ya nuna, Magatakardar makarantar na wancan lokaci, FC Mordi, ya aiko masa da takarda ranar 1 ga Nuwamba, 1995.

KU KARANTA: Malamai sun bayyana abin da za su yi idan Gwamnati ta gaza tsare Makarantu

An dakatar da Adekolawole daga aiki na watanni biyu a dalilin laifin da ya aikata, aka daina biyansa albashi, kuma aka sauke shi daga mukaman da ya ke a kai.

Duk tsawon wannan lokaci an san wannan Bawan Allah ne a makarantar da John Edaogbogun, sai a 2010 kwatsam ya canza sunansa, ya koma John Adekolawole.

Adekolawole ya gamu da fushin iyayen gidansa, aka ja-kunnensa da kyau kan ya guji aikata wannan mummunan aiki nan gaba, ko ayi masa hukunci mai tsanani.

Daga baya an bi an zare wannan takarda, ta yadda za a batar da maganar tamkar ba a taba yi ba.

KU KARANTA: Saurayi da Budurwan da su ke soyayya tun 1999 sun shirya yin aure

An taba dakatar da Adekolawole daga aiki a 1995 kafin zama Shugaban Poly, Ede
Takardar dakatar da John Adekolawole Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Adekolawole ya tabbatar da cewa an yi haka, a cewarsa an zare takardar ne bayan gano bai aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa ba, ya ce sharri ake nufe sa da shi.

A game da boye sunansa, malamin ya ce ya yi haka ne bayan kammala Digirin PhD a 2010, saboda wani malami ya fada masa ya cire Edaogbogun daga cikin sunansa.

Cikin makon nan ku ka samu labari cewa hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da fasaha (Polytechnic) ta Ede da ke Jihar Osun, ta dakatar da shugaban na ta.

An dauki wannan mataki ne bisa dogaro da dalilai 21 da ake zargin shugaban makarantar, Dr. John Adekolawole da aikatawa, daga ciki har da yin barci a cikin ofis.

A 2017, shugaba Muhammadu Buhari ya nada Adekolawole a matsayin shugaban makarantar koyon aikin na Ede wanda ya yi Digirinsa na BSc da MSc a 1982 da 1990.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel