Soyayyar da aka fara a shekarar 1999, za ta kai ga aure, jama’a sun tofa albarka

Soyayyar da aka fara a shekarar 1999, za ta kai ga aure, jama’a sun tofa albarka

- Wasu Masoya a Najeriya da su ka fara soyayya tun 1999 sun fito da hotunansu

- Wannan Saurayi da Budurwa sun dauki hotuna da ke nuna suna shirin yin aure

- Jama’a sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da soyayyar ta su mai shekaru 21

Wasu Bayin Allah sun kawo abin magana a dandalin sada zumunta yayin da su ka dauko labarin soyayyarsu da su ka fara tun a shekarar 1999.

Bayan tsawon shekaru su na cin budurci da samartaka wadannan Bayin Allah sun amince za su shiga daga ciki.

Mutane da dama sun yi mamakin jin yadda wadannan masoya su ka shafe shekaru sama da 20 su na soyayya da juna, amma ba su kai ga yin aure ba.

Wani mutumi mai suna Austine Bassey ne ya fara fito da wadannan masoya yayin da ya wallafa hotunansu a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

KU KARANTA: Auren mai mata karin lada ne - Budurwa

Mista Austine Bassey ya nuna tsofaffin hotunan masoyan wanda aka dauka shekaru 21 da su ka wuce, da kuma hotunan aure da aka dauka kwanan nan.

Bassey da kansa ya jinjina wa masoyan ganin sun yi shekara da shekaru ba su yaudari juna ba.

Ga kadan daga cikin abin da wasu ke fada:

“Ikon Allah, ba kasafai aka saba samun wannan ba. Tun 1999 suna tare, kuma mijin bai bada wani uzuri ya tsere ba, matar ta yi sa’a sosai." inji lori Dammy.

KU KARANTA: Ba a sa uwa a gidan aure

Soyayyar da aka fara a shekarar 1999, za ta kai ga aure, jama’a sun tofa albarka
Soyayyar da ta yi shekara 21 Hoto: Austine Bassey
Asali: Facebook

Ya ce yanzu wannan mutumi ya gaji da cin shinkafa, ya na so ya jarraba tuwon uwargida.

Ita kuwa wata mata cewa ta yi: “Tafiya ta yi tafiya, Ubangiji ya yi wa aurensu albarka, ya ba su kyawawan ‘ya ‘ya.”

Dazu kun ji cewa wata Dalibar Makaranta za ta yi kwana 1 a kan kujerar Gwamnan Legas. Mulkin jihar Legas zai fada hannun Budurwa bayan ta lashe wata gasa.

A gasar Spelling Bee na shekarar bana, Jemimah Marcus ce ta yi nasarar zuwa ta farko.

Miss Jemimah Marcus ta na karatu ne a makarantar Angus Memorial Senior High School, ta samu kyautar N250, 000 kuma an dauke mata kudin jami'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel