Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa

Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa

- NSMC ta ce matsalar rashin tsaro tana da alaka da rashin tsaron iyakokin Najeriya

- A cewar kungiyar, ya kamata a fara amfani da fasaha ta musamman wurin kula da iyakokin

- Sun sanar da hakan ne a wata takarda wacce Ambasada Sani Bala ya sanya hannu

NSMC ta kwatanta rashin tsaron Najeriya da rashin tsaron iyakoki, ta kara da cewa hakan ne dalilin da ya sanya Najeriya ta kasa cin nasara a kan 'yan bindiga da 'yan Boko Haram.

Ta ce matsawar gwamnatin tarayya tana son cin nasara a kan rashin tsaro ta wuraren tafkin Chadi, wajibi ne a kula kwarai, Daily Trust ta wallafa.

Wadannan suna kadan daga cikin hanyoyin da za a tsare 'yan Najeriya daga cutarwar 'yan bindiga, kamar yadda mambobin kwamitin suka tattauna don samar da tsaro a kasar nan.

KU KARANTA: Satar 'yan makarantan Kankara: Babu gwamnati a kasar nan, Ezekwesili

Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa
Iyakokin kasar nan da ke bude ke assasa rashin tsaro, Kwamitin arewa. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Wata takarda da Ambasada Sani Bala, daya daga cikin mambobin kungiyar ya sanya hannu a maimakon sauran mambobin, ta ce dakatar da shigo da makamai ta iyakoki ita ce babbar hanyar kawo karshen rashin tsaro.

"Duk da ana cewa an rufe iyakokinmu, amma duk da haka ya kamata a yi amfani da fasaha wurin kula da iyakokin. Babu dalilin da zai sanya a cigaba da zama haka nan, ana shigowa da kananu da manyan makamai kasar nan. Kullum matsalolin tsaro, ta'addanci da kashe-kashe sai kara yawa yake yi," kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: Kankara: Iyayen dalibai sun jeru a farfajiyar makaranta suna jiran dawowar 'ya'yansu

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta samar da wani kwamiti wanda zai dinga kulawa da tsayar da farashin man fetur.

Hakan ya biyo bayan sanar da sabon farashin mai na PMS da gwamnati tayi a makon da ya gabata, inda ta sanar da farashin a ranar Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin da gwamnatin tarayya, wanda NLC ta shirya da kungiyar kasuwanci don fitar da tsayayyen farashin man fetur, jaridar Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng