Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga

Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga

- Sanata Hanga na Kano ta tsakiya, ya ce Buhari yana tsoron juyin mulki ne shiyasa ya ki sauke shugabannnin tsaro

- Ya ce Buhari ba zai iya daura wadanda bai aminta dasu ba a shugabancin tsaro, don tsoron wadanda zai daura

- A cewarsa, kananun da zai daura za su iya cin amanar Buhari domin zai yuwu su wuce wadannan buri, tsaf za su iya sauke shi

Sanata Rufai Hanga ya yi hasashen dalilin da yasa shugaba Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro. Hanga ne sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar tarayya, ya sanar da Daily Sun dalilin da ya sanya Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro.

Mutane da dama sun yi ta caccakar Buhari saboda kin sauke shugabannin tsaro.

Sanatan ya ce Buhari yana tsoron kananan jami'an tsaron da zai daura a kan mulki ba za su iya mara masa baya kamar wadannan shugabanni ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar wakilai ta tsayar da fara daukar ayyuka 774,000

Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga
Tsoron juyin mulki yasa Buhari ya kasa sallamar shugabannin tsaro, Sanata Hanga. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Kamar yadda Hanga yace: "Mutane sun dade suna korafi a kan yadda Buhari ya kekashe kasa ya ki sauke shugabannin tsaro. Duk da kowa ya san Buhari baya gamsuwa da ayyukansu, amma ba shi da yadda zai yi. Idan ya saukesu, zai iya dauke wadanda suka fi su buri, za su iya hada kai su yi masa juyin mulki."

Yace, "Ba zai iya daura kowa a kujerun ba, sai amintattunsa. Amma kuma kin saukesu yana janyo cutarwa ga 'yan kasa da kasar gaba daya."

Sai dai majalisar tarayya ta zauna da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, bayan satar daliban GSSS Kankara, inda suka tattauna a kan yadda za su bullo wa harkar tsaro don a cetosu.

KU KARANTA: Da duminsa: CJN Tanko ya kamu da korona, baya Najeriya baki daya

A wani labari na daban, mazauna Gauca, wani kauye da ke Venezuela, sun tsinci tsadaddun abubuwa wadanda suka share musu hawaye a lokacin da kasar take fuskantar girgiza a tattalin arzikinta.

Wani mai kamun kifi, mai suna Yolman Lare yana zaune da iyalinsa cikin matsananciyar fatara, yayin da ya tsinci wani abu mai kyalli a bakin rafi.

Kamar yadda The New York Times ta ruwaito, lokacin da Lares yayi lalube a bakin rafin, sai ya dago wani dankwalelen zinari mai dauke da hoton Mary.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng