Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara

Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara

- Wata mata wacce ta shiga halin tashin hankali da takaicin rayuwa bayan an sace mata jika da yaronta a GSSS Kankara ta bayyana alhininta

- Ta ce tabbas mutuwa gaskiya ce, kuma har mahaifinta ya mutu ta hakura, amma wannan satar ta fi mutuwa rikitarwa

- Ta ce matsalar ita ce ba su san halin da yaransu suke ciki ba, saboda zaluncin 'yan bindiga shine babban abu mafi firgitarwa

Satar daruruwan daliban Kankara na jihar Katsina ya janyo alamomin tambaya a kan matsalar tsaro, wanda hakan ya rikita tunanin iyaye da dama, Daily Trust ta ce.

Daya daga cikin iyayen, Hajiya Marwa Hamza, wacce aka sace dan ta da jikanta a daren Juma'a, cikin GSSS Kankara, ta bayyana irin tashin hankalin da ta shiga.

A cewarta, "Ban taba shiga damuwa ba a rayuwata irin wannan. Na san yadda ake ji idan dan uwan mutum ya rasu, saboda na rasa mahaifina, kuma na san mutuwa dole ce, dole mutum yayi hakuri. Amma wannan ba kamar mutuwa bane, ba mu san halin da yaranmu suke ciki ba.

Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara
Ban taba shiga bakin cikin rayuwa kamar haka ba, Matar da aka sace danta da jikanta a Kankara. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar wakilai ta tsayar da fara daukar ayyuka 774,000

"Kanwata ce ta fara sanar da ni faruwar lamarin, bayan ta kirani a waya. Take a nan na kira DPO don ya san me ake ciki, sai dai ya sanar min da cewa sun je yin aiki wani wuri, amma za su yi gaggawar komawa.

"Har karfe 2 na dare, ban iya barci ba. Bayan na idar da sallar asuba sai nayi gaggawar tafiya zuwa makarantar, inda aka ce sojoji sun ceci wasu yaran. Mun yi gaggawar zuwa wurin sojojin, inda muka duba duk yaran, amma babu namu.

"Abinda ya fi batamin rai shine yadda kwamishinan ilimi yace ba a sace yaranmu ba, harbin bindigan da suka ji ne ya watsa su. Tabbas gwamna ya yi kokari, don har hawaye ya zubar a gabanmu, yana tabbatar mana da cewa zai yi iyakar kokarinsa, kuma yana nan yana yi. Amma maganganun kwamishinan nan ya yi matukar bata mana rai."

KU KARANTA: Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu

Daya daga cikin yaran da ya tsero yace akwai yara fiye da 500 a hannun 'yan bindigan.

Ta mika godiyarta ga gwamnan jiharsu, tace amma yana zagaye da wadanda basu fadi masa gaskiya, haka shugaba Buhari. Tace musamman yadda Garba Shehu ya lailaya karya ya watsa a duniya, har yana cewa dalibai 10 kadai aka sace.

A wani labari na daban, tsohuwar ministar kudi, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta roki gwamnatin tarayya da tayi gaggawar yin duk yadda za ta iya don dawo da fiye da dalibai 300 na GSSS Kankara, jihar Katsina, jaridar The Punch ta wallafa.

A cewarta, wajibi ne a dauki mataki a kan wadanda suke wasa da rayukan yaran. Ngozi, wacce ita ce 'yar takarar shugaban WHO mafi rinjaye, ta bayyana hakan a Twitter, jiya da daddare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel