'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa

'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa

- Kungiyar Dattijan Arewa ta bayyana cewa yan Najeriya basu more shugaban kasa ba, kuma sun bukaci da Buhari yayi murabus

- Kakain kungiyar Dr Hakeem Baba Ahmed, ya ce Shugaba Buhari yana Jihar Katsina aka sace 'yan makaranta amma ya gaza zuwa jajanta musu

- Baba Ahmed ya bayyana cewa Buhari baya wani yunkurin kawo karshen ta'addanci duba da yadda ya bar rundunar soji yadda take tun lokacin Jonathan ba tare da kara mata karfi ba

Dr Hakeem Baba Ahmed, mai magana da yawun kungiyar dattijan arewa, hulda da kuma bada shawarwari, ya bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin, wadda Legit.ng ta yi nazari inda Ahmed ya bayyana cewa, "yan Najeriya ba su more ba, sun samu shugaba mara tausayawa".

Kungiyar dattijan arewa (NEF) tayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da yayi murabus bisa kasa shawo kan matsalar tsaro a kasar bayan yin garkuwa da fiye da daliban sakandire 500 a jihar sa ta haihuwa.

'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa
'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa. Hoto: @NewsWireNGR
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

Baba-Ahmed ya damu akan Buhari. Yana mamakin yadda shugaban kasa duk da kasancewar shi a Daura lokacin da abin ya faru bai kai ziyarar jaje ga iyayen yaran da abin ya shafa ba, sai ma ya zauna a gidansa yana karbar baki.

"Ya zauna Daura, gwamnoni suna tururuwa don zuwa gaishe shi, kowa yaje fadar don bukatar shi, ina tausayin, ina hakkin shugabancin?, ta yaya zai nuna wa mutane tabbas ya damu"?.

Kungiyar, a rahoton da ta fitar ranar Talata, ta hannun shugaban hulda da jama'a da bada shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ta bayyana cewa yanzu ran dan Adam ya rasa kima karkashin mulkin Buhari, bisa rashin tabuka katabus a yakar ayyukan ta'addancin Boko Haram, da sauran miyagun laifuka kamar garkuwa da mutane, bindiga dadi da kuma satar shanu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

A hirar da yayi ranar Laraba, Dr Ahmed ya ce, "daruruwan yan makaranta aka yi garkuwa dasu, watakila yan bindiga dari da hamsin ne suka ratsa gari a kan babura, suka shiga makaranta, ba tare da an dakatar da su ko wani yunkurin hakan ba, suka yi nasarar debe su."

"Ina jami'an tsaron wajen suke, ta yaya bayan kwana biyar da kwashe su har yanzu ba labarin su. Kwata kwata ba a takurawa yan ta'adda, kullum kara sace mutane ake yi, garkuwa da mutane kara zama ruwan dare ya ke yi".

"Baba Ahmed ya kuma yi magana akan karfin rundunar soji, "bamu ga Buhari ya kara yawan su ba, ko ya kara musu karfi ba, ko an kara musu makamai ba, yadda Jonathan ya tafi ya barsu har yanzu haka suke, ba abin da ya yi, nan aka sace dalibai a jihar da yake, ka iya cewa a kusa da shi. Bai je Katsina don binkica abin da ya faru ba, bai je Kankara ba, wadda ke kudancin jihar don jajantawa al'umma ba."

"To, ku sani wanda yake mulkar ku mutum ne da bashi da nuna kula ko damuwa ko daukar mataki akan abubuwan da suke faruwa ba. Yan Najeriya suna zaune ne kara zube, ba mulki ake ba".

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel