Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu

Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu

- Mazauna Gauca, wani kauye da ke Venezuela sun more bayan sun tsinci dunkulen zanarai har da zobuna

- Wani Lare, mai kamun kifi, shine ya fara tsintar dunkulen zinaren a bakin rafi, kafin sauran 'yan kauyen su biyo baya

- Mutumin mai iyalai, ya yi farin ciki har da hawaye, saboda tunda yake a rayuwarsa bai taba cabawa irin haka ba

Mazauna Gauca, wani kauye da ke Venezuela, sun tsinci tsadaddun abubuwa wadanda suka share musu hawaye a lokacin da kasar take fuskantar girgiza a tattalin arzikinta.

Wani mai kamun kifi, mai suna Yolman Lare yana zaune da iyalinsa cikin matsananciyar fatara, yayin da ya tsinci wani abu mai kyalli a bakin rafi.

Kamar yadda The New York Times ta ruwaito, lokacin da Lares yayi lalube a bakin rafin, sai ya dago wani dankwalelen zinari mai dauke da hoton Mary.

Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu
Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu. Hoto daga newyorktimes.com
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2

Tun bayan nan, da yawa daga cikin 'yan kauyen sun tsinci a kalla abu daya na zinari, yawanci zobuna.

Wasu daga cikin 'yan kauyen sun sayar da zoben da suka tsinta $1,500, wanda yayi daidai da N570,375.

'Yan kauyen sun fuskanci wahalhalun rayuwa, amma bayan 'yan tsince-tsincen da suka yi, sun samu sassauci.

Kamar yadda Lare yace: "Fara girgiza dunkulen zinaren nayi, sai kuma wani kukan hawaye ya fara zubo min. Wannan shine karo na farko da na samu abu mai daraja a rayuwata."

Ya ce Ubangiji ne ya taimake shi ya kawo masa dauki.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a kan rashin lafiyan CJN bayan bai halarci rantsar da sabbin SAN ba

A wani labari na daban, hakan ya biyo bayan sanar da sabon farashin mai na PMS da gwamnati tayi a makon da ya gabata, inda ta sanar da farashin a ranar Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin da gwamnatin tarayya, wanda NLC ta shirya da kungiyar kasuwanci don fitar da tsayayyen farashin man fetur, jaridar Punch ta wallafa.

A ranar 8 ga watan Disamba an rage farashin man fetur da N5, maimakon N168 zuwa N162.44 kowacce lita tun daga ranar 14 ga Disamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng