Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG

Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG

- Tsohuwar ministar kudi, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ta roki gwamnatin tarayya a kan tayi iyakar kokarinta wurin ceto daliban Katsina

- A cewarta, yakamata a damki duk wadanda suke da hannu a kan wasa da rayukan yara fiye da 300, kuma a yi musu hukunci da ya dace dasu

- Ngozi, wacce ita ce 'yar takarar shugabancin WHO mafi rinjaye, ta wallafa hakan a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, jiya da daddare

Tsohuwar ministar kudi, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta roki gwamnatin tarayya da tayi gaggawar yin duk yadda za ta iya don dawo da fiye da dalibai 300 na GSSS Kankara, jihar Katsina, jaridar The Punch ta wallafa.

A cewarta, wajibi ne a dauki mataki a kan wadanda suke wasa da rayukan yaran. Ngozi, wacce ita ce 'yar takarar shugaban WHO mafi rinjaye, ta bayyana hakan a Twitter, jiya da daddare.

KU KARANTA: Da duminsa: CJN Tanko ya kamu da korona, baya Najeriya baki daya

Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG
Kankara: Ku dawo mana da yaranmu maza, Okonjo Iweala ga FG. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Kamar yadda ta wallafa: "Hakika satar fiye da dalibai 300 na jihar Katsina, abu ne mai razanarwa. Ina matukar taya 'yan uwan yaran alhini a kan faruwar lamarin. Kuma wajibi ne hukuma tayi gaggawar kwato yaran. Kuma wajibi ne a hukunta duk wadanda aka kama da hannu a kan wasa da rayuwar yaranmu."

KU KARANTA: FG ta nada sabon kwamitin tantance farashin man fetur, za a samu sabon farashi

A wani labari na daban, majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da fara daukar ma'aikata 774,000 na ayyuka na musamman da za ta fara a watan Janairun 2021.

Majalisar kuma ta bukaci ma'aikatar kudi da ta dakatar da sakin kudaden da ya kamata a yi amfani dasu don shirin har sai an kammala bincike a kan wasu matsaloli da suka taso na ingancin shirin.

Hon. Olajide Olatubonsun ya daga batun a majalisar saboda ya shafi al'umma, sannan majalisar ta kunshi sauke shugaban NDE, Mohammed Kadan Argungu, inda tace a yi gaggawar mayar dashi mukaminsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng