Da duminsa: Majalisar wakilai ta tsayar da fara daukar ayyuka 774,000

Da duminsa: Majalisar wakilai ta tsayar da fara daukar ayyuka 774,000

- Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dage shirin NDE na daukar ma'aikata na musamman guda 774,000

- Dama ya kamata a fara shirin a watan Janairun 2021, amma majalisar ta bukaci dagewa saboda wasu dalilai

- Sannan ta bukaci gwamnatin tarayya tayi gaggawar mayar da shugaban shirin, ta ce batun cireshi gurguwar shawara ce

Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da fara daukar ma'aikata 774,000 na ayyuka na musamman da za ta fara a watan Janairun 2021.

Majalisar kuma ta bukaci ma'aikatar kudi da ta dakatar da sakin kudaden da ya kamata a yi amfani dasu don shirin har sai an kammala bincike a kan wasu matsaloli da suka taso na ingancin shirin.

Hon. Olajide Olatubonsun ya daga batun a majalisar saboda ya shafi al'umma, sannan majalisar ta kunshi sauke shugaban NDE, Mohammed Kadan Argungu, inda tace a yi gaggawar mayar dashi mukaminsa.

Da duminsa: Majalisaar wakilai ta tsayar da fara ayyuka 774,000
Da duminsa: Majalisaar wakilai ta tsayar da fara ayyuka 774,000. Hoto daga @thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta

Hon. Onofiok Luke ya ce an baiwa gwamnatin tarayya gurguwar shawara ta hanyar sauke shugaban NDE daga mukaminsa, inda yace ya yi iyakar kokarinsa ne don tabbatar da shirin ya samu nasara.

A cewarsa, akwai bukatar a dakatar da shirin saboda akwai matsalolin da suka shafi inganci da bukatar gina ma'aikatu.

Kamar yadda yace, DG ya tsaya a kan gaskiya kuma batun saukesa daga mukaminsa, gurguwar shawara ce. Inda yace dama ya kamata a fara shirin a 2020 ne, an samar da kudin shirin a kasafin 2020. Amma sai aka matsar dashi zuwa 2021, don haka wajibi ne dage shirin har sai an sama masa gurbi a kasafin 2021.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta samar da wani kwamiti wanda zai dinga kulawa da tsayar da farashin man fetur.

Hakan ya biyo bayan sanar da sabon farashin mai na PMS da gwamnati tayi a makon da ya gabata, inda ta sanar da farashin a ranar Litinin.

Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin da gwamnatin tarayya, wanda NLC ta shirya da kungiyar kasuwanci don fitar da tsayayyen farashin man fetur, jaridar Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel