Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce

Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce

- Sanata Dino Malaye ya saki wani bidiyonsa yana tikar rawa, wanda hakan ya janyo cece-kuce

- Tsohon sanatan ya yi bidiyon ne a tsakiyan larabawa a hamada, ga dukkan alamu yana cikin nishadi

- Mabiyansa sun yi ta kallon bidiyon, inda kowa yake tofa albarkacin bakinsa a kan dan siyasan

Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta kudu, Dino Melaye, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani bayan ya saki bidiyonsa yana kwasar rawa a tsakiyar hamada.

An san sanatan da nishadantar da mabiyansa da wakoki da raye-raye masu burgewa. Kuma yana wallafa su ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Anga tsohon sanatan a hamada tare da wasu larabawa yana kwasar rawa. Mutane da dama sun je kasan wallafar tasa suna tofa albarkatun bakinsu.

Wata bennylyon1 cewa tayi: "Kada mutum ya kuskura ya bar kunci da takaici su dame shi, hasali ma, farinciki da nishadi shi yafi."

Wani IcePrint2 yace: "Muna fatan Ubangiji yayi maka jagora. Mu masu kaunar ka ne har abada."

KU KARANTA: Tubabben Boko Haram ne ya halaka kanal din soja, Sanata Ndume

Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce
Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce. Hoto daga @dino_melaye
Asali: Twitter

KU KARANTA: Uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta bukaci a yi wa Najeriya addu'a

A wani labari na daban, KADRIS ta ce za ta fara amsar N1000 don cigaban jihar na 2021 daga hannun duk wanda ya mallaki hankalin kansa, kuma mazaunin jihar Kaduna daga ranar Laraba.

Hakan zai cigaba ne duk shekara, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna, inda yace daga shekarar 2021, duk wani mai hankalin kansa da yake zaune a jihar wajibi ne ya biya wannan harajin.

Ya ce hakan yayi daidai da sashi na 9 (2) na dokar amsar harajin jihar Kaduna na 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel