Pfizer/BioNTech: Za a samar da kwayar maganin COVID-19 miliyan 40 a 2020

Pfizer/BioNTech: Za a samar da kwayar maganin COVID-19 miliyan 40 a 2020

-Kamfanin Pfizer/BioNTech ya kammala aikinsa kirkiro maganin cutar COVID-19

-An fara raba wannan kwayoyin magani ga wadanda su ka kamu da Coronavirus

-Gwamnatin Amurka za ta aikawa kasashe maganin domin a samu saukin cutar

A ranar Lahadi, 13 ga watan Disamba, 2020, kasar Amurka ta fara rabon sabon maganin Coronavirus da kamfanin Pfizer/BioNTech ya kirkiro.

Hukumar dillacin labarai tace hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan wannan magani ya samu amincewar ayi amfani da shi a matsayin na gaggawa.

Wannan mataki da Amurka ta dauka zai taimaka wajen yakar wannan muguwar cutar numfashi wanda duk ranar Duniya sai ta kashe Amurkawa 2, 000.

Hukumomi sunce gwamnati tana kokarin yi wa mutane akalla miliyan 100 ko kuma 30% na al’ummar kasar Amurka rigakafin wannan cuta nan da 2021.

KU KARANTA: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19

Gidan labarai na Reuters yace an cika wata mota makil da wannan magani daga kamfanin Pfizer da ke Kalamazoo, Michigan, a ranar Lahadi da yamma.

Za a fara aiki da wannan sabon magani a fadin Duniya, ma’aikatan asibiti; likitoci da malaman jinya za a soma ba maganin saboda sun fi fuskantar barazana.

Gwamnatin tarayyar Amurka ta na kokarin ganin yadda za a kai wannan magani zuwa wurare 600 a Duniya ta karkashin shirin Operation Warp Speed.

Darektan wannan shiri, Dr. Moncef Slaoui, ya shaidawa Fox News cewa suna harin samar da kwayoyi miliyan 40 na maganin nan da karshen bana.

KU KARANTA: An yi karya game da asalin kwayar COVID-19

Pfizer/BioNTech: Za a samar da kwayar maganin COVID-19 miliyan 40 a 2020
Maganin COVID-19 Hoto: www.reubenabati.com.ng
Asali: UGC

Magungunan da za a samar a shekarar bana, za su isa ayi amfani da su a kan mutum miliyan 20.

A wata jiya ne kamfanonin Pfizer da na BioNTech su ka tabbatar da cewa an samu riga-kafin COVID-19 wanda yanzu ta harbi miliyoyin mutane a Duniya.

Kamar yadda suka bayyana, an gwada rigakafin a kasashe shida. Wannan magani ya na aiki kamar yadda binciken da aka yi kan mutum 43, 5000 ya nuna.

Ana tsammanin cewa samun wannan rigakafin zai zamo wata hanyar samun sakat a Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng