Manyan nade-nade guda 8 da Shugaba Buhari yayi a 2020

Manyan nade-nade guda 8 da Shugaba Buhari yayi a 2020

- Abune da yake sananne cewa yan Najeriya da dama sun rasa ayyukansu tun daga watan Maris lokacin da annobar Korona ta bulla a kasar

- Sai dai an yi wasu nade-naden mukamai musamman daga bangaren yan siyasa a wasu hukumomin ma’aikatu

- A wannan zauren, Legit.ng ta bduba wasu manyan nade-nade takwas da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi duk da wahalar da aka shiga saboda korona a 2020

1. Farfesa Ibrahim Gambari

A ranar 13 ga watan Mayu, Farfesa Gambari ya zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya kasance dan diflomasiyya kuma gogagge a fannin ilimi.

Ya maye gurbin Mallam Abba Kyari wanda ya mutu sakamakon cutar korona a watan Afrilu.

Manyan nade-nade guda 8 da Shugaba Buhari yayi a 2020
Manyan nade-nade guda 8 da Shugaba Buhari yayi a 2020 Hoto: The nation, Vanguard.
Source: UGC

2. Yakubu Mahmood

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Farfesa Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), karo na biyu a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba.

An gudanar da taron rantsarwar kafin fara zaman majalisar zartarwa na mako-mako, a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.

KU KARANTA KUMA: Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara

A ranar 1 ga watan Disamba ne majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Yakubu a matsayin shugaban INEC, karo na biyu.

3. Olalekan Fadolapo

Shugaban kasar ya nada Fadolapo a matsayin shugaban hukumar tallace-tallace ta kasa wato APCON a ranar 26 ga watan Agusta.

4. Buki Ponle

A ranar 27 ga watan Agusta, Shugaba Buhari ya amince da nadin Buki Ponle a matsayin Manajan Darakta na kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN).

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara

5. Muhammadu Alhaji Muhammed

A ranar 2 ga watan Mayu, shugaban kasar ya amince da nadin AVM Muhammadu Alhaji Muhammed (Rtd.) a matsayin sabon darakta janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA).

6. Alwan Hassan

A ranar 4 ga watan Yuni, shugaban kasar ya amince da nadin Alwan Ali Hassan a matsayin mukaddashin manajan darakta na bankin gona (BOA).

7. Suleiman Abba

A ranar 26 ga watan Mayu, tsohon sufeto janar na yan sandan ya zama shugaban kwamitin amintattu na asusun rundunar sojin Najeriya (NPTF).

8. Ahmed Kuru

Shugaban kasa Buhari ya sake nada Ahmed Kuru a matsayin manajan darakta na hukumar AMCON zangon karshe na shekaru biyar a ranar 7 ga watan Disamba.

A wani labarin, wasu mambobin majalisar wakilai guda biyu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yau Talata, 15 ga watan Disamba.

Yan majalisar sun sanar da shawarar da suka yanke a cikin wasu wasiku mabanbanta wanda kakakin majalisar ya karanto a zauren majalisar.

Yan majalisar sune Datti Yako daga jihar Kano da kuma Danjuma Usman Shiddi daga jihar Taraba, kuma dukkaninsu sun daura alhakin sauya shekarsu kan rikicin shugabanci da ake fama dashi a jam’iyyunsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel