Da duminsa: Kamfanin Pfizer ya samar da riga-kafin cutar korona
- Kamfanonin Pfizer da na BioNTech sun tabbatar da samar da riga-kafin cutar korona
- Kamar yadda suka bayyana, riga-kafin an gwada shi a kasashe shida a fadin duniya
- An gwada shi a kan mutum 43,500 inda aka san yana bai wa a kalla mutum kashi 90 kariya
Kamfanin Pfizer da BioNTech ta ce ta samar da riga-kafin cutar korona na farko da zai iya bai wa a kalla kashi 90 na jama'a kariya daga samun cutar.
Kamar yadda The Cable ta wallafa, an gwada riga-kafin a kan mutum 43,500 a kasashe shida kuma babu wata matsala da aka samu.
Ana bada riga-kafin sau biyu amma makonni uku tsakani, kamar yadda aka gwada a Amurka, Jamus, Brazil, Argentina, South Afrika da Turkiyya. Hakan ya nuna cewa, ana samun kariya daga cutar bayan mako daya da amfani da shi.
Ana tsammanin samun wannan riga-kafin zai zamo wata hanyar samun sakat ta duniya bayan barnar da cutar ta dade tana yi.
KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya yi magana a kan fastocinsa na takarar shugabancin kasa
Najeriya da wasu kasashe masu tarin yawa sun saka takunkumi a matsayin hanyar dakile yaduwar cutar wacce ta kashe mutum 1,263,787 a fadin duniya.
Kamar yadda Pfizer tace, za ta samar da riga-kafin da zai isa mutum miliyan 50 zuwa karshen 2020 kuma za ta kai har 1.3 biliyan zuwa karshen 2021.
KU KARANTA: Magidanci ya yi basaja a kafar sada zumunta, ya nemi lalata da matarsa, ta amince
A wani labari na daban, wasu malamai 5 da dalibi daya, sun kamu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare da ke jihar Legas. Gwamnatin jihar Legas ta sanar da hakan a ranar juma'a, jaridar The Punch ta wallafa.
Kamar yadda takardar mai taken jihar Legas ta tabbatar da samun wasu masu cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare kuma kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng