Sin ta yi karya game da inda aka samo salin kwayar cutar COVID-19 – Rahotanni

Sin ta yi karya game da inda aka samo salin kwayar cutar COVID-19 – Rahotanni

Wani danyen rahoto mai ban kyama da aka fito da shi kwanan nan ya nuna cewa kasar Sin ta boye gaskiyar lamarin cutar COVID-19 wanda ake zargin ya samo asali ne daga yankin.

Jaridar Daily Nigerian ta ce wannan rahoto da ‘Five Eyes’ ta fitar ya bayyana cewa Sin ta yi wa Duniya karya game da yadda ake kamuwa da cutar COVID-19 tsakanin mutum da mutum.

Kasar ta kuma ki mikawa kasashen Turai samfurin wannan kwayar cuta ta COVID-19 domin su fara aikin kirkiro maganin cutar da yanzu ta kama mutane kusan miliyan uku da rabi.

Mahukuntar Kasar ta Sin sun kuma yi kokarin toshe duk wani labari da aka yi yunkurin fitarwa game da bakuwar cutar. Jaridar New York Post ta fitar da rahoton wannan binciken.

New York Post ta Amurka ta fallasa cewa COVID-19 ya fito ne daga Sin. Jaridar ta wallafa rahoton da ya ce kwayar cutar ta barko ne daga makarantar nazarin cututtuka da ke garin Wuhan.

A baya an yi watsi da rahotannin da su ke bayyana cewa cutar COVID-19 ta fito ne daga garin Wuhan. Sabon binciken da aka yi ya ce akwai kanshin gaskiya a wannan rahoton.

KU KARANTA: Manyan Taurarin kwallon Duniya da su ka kamu da cutar COVID-19

Sin ta yi karya game da inda aka samo salin kwayar cutar COVID-19 – Rahotanni

Ana zargin a Garin Wuhan aka cire cibiyar cutar Coronavirus
Source: Twitter

“Wani babban jami’in da ke bincike ya shaidawa Fox News cewa mafi yawan hukumomin bincike sun yarda cewa COVID-19 ta fito ne daga wani dakin nazarin cuttuka da ke Garin Wuhan.”

Majiyar ta ce an yi kuskure ne wajen fito da wannan kwayar cuta wanda ya barke ya shiga kasashe.Yanzu cutar ta kashe mutane fiye da 250, 000, daga ciki akwai 85 a Najeriya.

Kasashen Amurka, Ingila, Australiya, New Zealand da Kanada ne su ka hadu su ka yi wannan bincike. Kasashen Ingilishin duk sun zargi Sin da kin fitowa ta fadawa Duniya gaskiya.

Rahoton ya ce: “Bincike ya nuna cewa Sin ta samu hujjar da ke nuna COVID-19 ta na yaduwa tsakanin mutum da mutum tun a farkon Disamba amma ta cigaba da karyata wannan.”

Bayan haka kasashen sun gano cewa Sin ta hana mutane shigo mata cikin kasa tuni, amma kuma ta cigaba da yaudarar sauran mutane da cewa babu bukatar su rufe kasashensu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel