Nesa ta zo kusa: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19

Nesa ta zo kusa: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19

Kungiyar farfesoshi daga sashen hada magunguna na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta ce ta samo maganin cutar coronavirus.

A yayin zantawa da jaridar Daily Trust a ranar Laraba, daya daga cikin masu binciken, Farfesa Haruna Abdu Kaita, ya ce sun samo maganin cutar COVID-19 daga tsirrai da ake samu a wasu sassan kasar nan.

Wannan labarin na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin shigo da maganin korona na gargajiya wanda kasar Madagascar ke amfani da shi don riga-kafi da kuma maganin cutar.

Nesa ta zo kusa: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19
Nesa ta zo kusa: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jama'a da dama sun kalubalanci hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari ciki har da kungiyar masu hada magunguna ta Najeriya.

Sun kwatanta hakan da cin zarafi ko tozarci ga masu hada magunguna, masana kimiyya da kuma masu bincike.

Kaita ya ce nan ba da dadewa ba za su fitar da maganin bayan sun tabbatar da nasararsa wajen kashe kwayar cutar a jikin dan Adam.

Ya ce bayan sun fitar da maganin, za su sanar da kowa tsirran da suka yi amfani dasu.

"Mu ba 'yan kasuwa bane don haka ba za mu boye komai ba. Za mu sanar da dukkan itatuwa da tsirran da muka yi amfani da su.

"Za mu yi hakan ne don masana kimiyya na fadin duniya su duba maganin sannan su yi kalubale idan akwai.

"Abinda nake nufi shine, duk abinda muka yi amfani da shi za mu bayyana."

KU KARANTA KUMA: Gambari: Abinda 'yan Najeriya za su yi tsammani daga gareni

Kaita ya ce, abu daya da za su boye shine yawan kowanne icce ko tsirran da suka yi amfani da su don samar da maganin.

Wannan a cewarsa, za su adana shi a matsayin saninsu su kadai.

Ya kara da cewa, tsohon shugaban jami'ar, Farfesa Abdullahi Mustapha yana daga cikin kungiyar.

An gano cewa, wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka san da maganin na ta kokarin samunsa tun kafin kungiyar ta fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel