Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta

Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta

- Kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun sace daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, wani mutum ya bayyana dalilin satarsu

- Mutumin ya ce 'yan bindigan sun dauki fansa ne a kan harin da 'yan sa kai suka kai musu, har suka ragargajesu

- A cewarsa, 'yan sa kai sun samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda da kuma raunana wasu ana saura mako 1 al'amarin ya faru

Bayan 'yan kwanaki da 'yan bindiga suka sace daliban jihar Katsina, wani mazaunin inda al'amarin ya faru, karamar hukumar Kankara, ya bayyana dalilan da suka janyo 'yan ta'addan suka aikata mummunan al'amarin.

Channels TV ta ruwaito yadda mazaunin, wanda ya bukaci a boye sunansa yace satar daliban GSSS Kankara, daukar fansa ne.

Kamar yadda yace, 'yan bindiga sun kaiwa kauyen 'Yar-Kuka farmaki a makon da ya gabaci wanda za a sace yaran, inda suka kashe wasu 'yan kauyen kuma suka tafi da wasu.

Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta
Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta. Hoto daga Vincent Obadofin
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona

Sai da 'yan sa kai suka shirya tsaf, tukunna suka binciki maboyar 'yan bindigan suka karkashesu, yayin da suka ji wa wasu daga cikinsu miyagun raunuka.

A cewarsa, ragargazar da 'yan sa kai suka yi musu shi ya janyo suka zagayo suka tsere da yaran makarantar a daren Juma'a, 11 ga watan Disamba.

Mutumin ya ce sai da 'yan bindigan suka kwashe yaran tsaf, suka tafi dasu kauyen Pauwa, inda suka ajiye baburansu. Amma sanin asalin yawan daliban da 'yan bindigan suka tsere dasu shine babban aiki.

KU KARANTA: Satar daliban Katsina: PDP ta magantu a kan watsa wa iyayen yara barkonon tsohuwa

A wani labari na daban, babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman, Garba Shehu, ya ce rundunar soji ta zagaye wadanda suka yi garkuwa da daliban jihar Katsina.

Shehu ya bayyana wa BBC hakan a ranar Lahadi, inda yace daliban da aka samu a hannun 'yan ta'addan sun yi kasa da yawan yadda ma'aikatan makarantar suka bayar da rahoto.

Dama a ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka ratsa wata makarantar sakandare ta kimiyya ta gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da wasu dalibai. Sun sace mafi yawan daliban cikin makarantar mazan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel