Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2

Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2

- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da majalisar jiharsa a kan tafiyarsa

- Ya sanar da hakan a wata wasika da tazo daga wurinsa, kuma kakakin majalisar ya karanta

- A cewarsa, zai je Amurka don duba lafiyarsa daga Lahadi, 13 ga watan Disamba zuwa Asabar, 28 ga watan

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana wa 'yan majalisar jiharsa batun tafiyarsa zuwa Amurka don duba lafiyarsa, daga ranar Lahadi, 13 ga watan Disamban 2020 zuwa ranar Asabar, 29 ga watan Disamban 2020, jaridar News wire ta wallafa.

Kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi ya karanta wasikar gwamnan zuwa 'yan majalisar tasa. Kamar yadda takardar tazo da taken, 'Sanarwa a kan tafiyata zuwa Amurka'.

Kamar yadda takardar tazo, "Ina son sanar da Rt Hon Speaker cewa zan je Amurka don duba lafiyata daga ranar Lahadi 13 zuwa Asabar, 29 ga watan Disamban 2020.

KU KARANTA: Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'

Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2
Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2. Hoto daga @Newswirengr
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi

"Idan na tafi, mataimakin gwamna zai cigaba da jagorantar ayyukan jihar har sai na dawo."

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, jam'iyyar PDP ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan amfani da barkonon tsohuwa wurin korar iyayen daliban makarantar sakandaren karamar hukumar Kankara, jihar Katsina, wadanda suka yi zanga-zanga a kan garkuwa da yaransu da aka yi.

A wata takarda da kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondigan ya saki, ya ce an nuna wa iyayen rashin imani kwarai da rashin tausayi karara, duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin jihar, amma duk da haka bai iya kare yaransu daga 'yan ta'addan ba.

Dama a ranar Juma'a 'yan bindiga suka je wata makaranta a jihar Katsina, duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je hutu jiharsa, inda suka yi awon gaba da dalibai 600; al'amarin da ya janyo cece-kuce iri-iri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel