APC ta fara rijistar mambobinta tare da tantance ƴan jam'iyya

APC ta fara rijistar mambobinta tare da tantance ƴan jam'iyya

- Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa ta tsayar da ranar 12 ga watan Disamba domin fara rijistar sabbi da sabunta rijistar tsofin mambobinta

- Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, ya bukaci tsofin mambobi su sabunta rijistarsu a mazabunsu

- Buni, gwamnan jihar Yobe, za su cigaba da fitar da sanarwa akai akai dangane da rijistar mambobin APC

Kwamitin kula da tsare - tsare na jam'iyya mai mulki, APC, sun ce sun kammala duk shirye-shirye don fara aiwatar da sabuwar rijista da sabunta rijistar ƴan jam'iyya daga ranar 12 ga watan Disamba.

Shugaban kwamitin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a sanarwar da suka fitar a birnin tarayya, Abuja, ranar Litinin bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, wanda suka haɗa da Shugaba Muhammad Buhari.

Ya ce za'a fara rijistar shaidar zama ɗan jam'iyya daga ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020 zuwa Asabar, 9 ga watan Junairu, 2021.

KARANTA: Garba Shehu: An yi min mummunar fassara, ba'a fahimci kalamaina da kyau ba a kan kisan manoma

"Mu na gayyatar dukkan ƴan jam'iyyarmu da su sabunta shaidarsu a mazaɓunsu.

"Haka zalika muna kira da ƴan jam'iyya da basu da rijista da suyi amfani da wannan damar don zama cikakkun ƴan jam'iyyarmu.

APC ta fara rijistar mambobinta tare tantance ƴan jam'iyya
APC ta fara rijistar mambobinta tare tantance ƴan jam'iyya @Thecable
Asali: Twitter

"Za'a gudanar da rijistar a dukkan mazaɓun ƙasar nan. Za'a kammala kai kayan rijista da sauran kayayyakin aiki zuwa kowacce jiha da ƙananan hukumomi kafin ranar 12 ga watan Disamba, 2020.

KARANTA: Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari yayin da ya ke zargin FG da daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki

"Mu na kira ga Shugabannin jihohi, ƙananan hukumomi da mazaɓu su ɗauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar cewa al'amurra sun tafi cikin tsari da daidaito yayin gudanar da rijistar.

"Za mu cigaba da bada bayanai akai akai" a cewar gwamna Buni.

A makon da ya gabata ne Legit.ng Hausa ta rawaito Buni na cewa nan bada dadewa ba jam'iyyar APC za ta tashi wata guguwar siyasa da za ta girgiza Najeriya.

Buni ya bayyana hakan ne bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC sun gana a sirrance da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng