Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'

Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'

- An yankewa wani fasto ma'aikacin gwamnatin London hukuncin shekara 9 a gidan gyaran hali

- Ana zarginsa da sata da kuma damfarar £41,000,000 daga cikin kudaden wurin aikinsa

- Kudaden da ake zargin ya kashe wa matarsa da karuwansa guda 4 saboda rashin daraja

Kamar yadda Mail Online ta ruwaito, wanda ake zargin, manajan wata makaranta, ya kashe £4,100,000 a kan mata 4, ciki har da matarsa da karuwansa.

Ya fara aiki a Haberdasher, wacce take da jibi da makarantun gwamnati masu irin sunanta a 1997, The Cable ta wallafa.

Thacker ya ce a 2006, Kayode ya fara amfani da tsarin tura kudi na BACS wurin hankada wa matarsa Grace kudade, zuwa asusunta. Daga nan ya koma kashe £98,000 duk wata.

Ya yi amfani da kudaden wurin kula da lafiyar matarsa Grace, har sai da ta mutu tana da shekaru 53 a 2013, sannan ya sanya hannu a wata takarda ta sana'a da Halima da wasu Toyin Lawal da Yetunde Turtak, masu sana'ar hayar gidaje.

KU KARANTA: FG: Najeriya za ta karba riga-kafin korona miliyan 20

Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'
Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Kayode ya ce karya yayi a kan batun auren Halima, sannan ya musanta lalata da sauran matan.

A gidanta dake Northfleet, Kent, Lawal mai shekaru 50 tace idan ta rasa kudin biyan haya, Kayode ne yake biya mata hayar a matsayinsa na faston wata coci a Najeriya.

Sannan an samu labarin yadda ya siya motoci na gani da fadi, kamar Mercedes, Audis da Infiniti, sannan ana zarginsa da tura kudade masu yawa zuwa Najeriya.

Duk shekara ana biyan mutumin mai yara 4, £57,000, sannan an kama shi da satar £150,000 da damfara, £3,950,000

"Yanzu haka an yanke wa maci amanar hukuncin shekaru 9 a gidan gyaran hali sakamakon satar £4,100,000 na kudin haraji da kuma kashewa mata 4 kudade masu yawa," kamar yadda jaridar ta wallafa.

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Najeriya na daya daga cikin zakakuran soji a Afrika, Magashi

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya miki sakon taya murnarsa ga Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo bisa samun nasarar lashe zabe da yayi, The Cable ta wallafa.

Akufo-Addo, wanda ya tsaya takara karkashin jam'iyyar NPP, kuma ya samu kuri'u 6,730,430, inda ya kayar da babban abokin takararsa tsohon shugaban kasa John Mahama, kuma dan takara karkashin jam'iyyar NDC wanda ya samu kuri'u 6,214,899.

A wata takarda ta ranar Alhamis, wacce Garba Shehu, Kakakin shugaban kasa ya saki, ya ce Shugaba Buhari ya baiwa sauran 'yan takara hakuri, sannan ya shawarcesu da su fara sanya kasarsu a gaba, su kuma tabbatar da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel