Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi

Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi

- Gwamnan jihar Ekiti zai dauki tsattsauran mataki a kan ma'aikatan gwamnati masu tozarta dokokin COVID-19

- Gwamnan yace wajibi ne duk wasu 'yan siyasa da ma'aikatan jiharsa su dinga amfani da takunkumin fuska

- Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, bayan ya lura da yawan masu cutar COVID-19 sun kai mutane 388 a jiharsa

A wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Ekiti Biodun Oyebanji ya saka hannu, gwamnan jihar ya zargi ma'aikatan gwamnatinsa da karya dokokin kare kai daga COVID-19.

"Duk da kowa ya san akwai annobar cutar COVID-19, mun lura da yadda ma'aikatan gwamnati da dama suke watsi da gaskiya suna yin yadda suka ga dama," kamar yadda takardar tazo.

"Wannan halayyar ba za ta haifar da d'a mai ido ba, kuma alama ce ta rashin sanin ciwon kai.

"Muna so ku sani, Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya ja kunnen duk 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnatin jiharsa, inda yace za a dauki mataki a kan wadanda ba su saka takunkumin fuska," yace.

KU KARANTA: Ba mu gayyaci Buhari don kure shi ba, Kakakin majalisar wakilai

Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi
Gwamnan APC zai dauka mataki a kan masu mukami a gwamnatin marasa saka takunkumi. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Ya fadi hakan ne bayan yadda yawan masu cutar COVID-19 suka karu zuwa mutane 388 a cikin jiharsa a ranar Alhamis, The cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Zukekiyar budurwa ta rasu ana sauran kwanaki kadan aurenta

A wani labari na daban, ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi, ya ce sojojin Najeriya suna daga cikin sojoji mafi nagarta a Afirka. Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, inda yace suna da damar kawo karshen duk wani makiyi idan aka ba su damar yin hakan.

A cewar Magashi, rundunar soji za ta iya kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabas, saboda sun ci nasara a yakin da suka je cikin wasu kasashen ketare.

A cewarsa, "A Afirka, ya kamata sojojin Najeriya su zama na daya a kwazo, saboda mun dade muna samun nasarori har a kasashen ketare. Mun je ECOMOG, mun yi iyakar kokarinmu. Mun je Sierra Leone, mun ci nasara. Amma sakamakon dadewar wannan yakin, mutane har sun gaji."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng