Rundunar 'yan sanda ta kira Sheikh Jingir don sake amsa tambayoyi a kan saba dokar jiha

Rundunar 'yan sanda ta kira Sheikh Jingir don sake amsa tambayoyi a kan saba dokar jiha

Rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta kira shugaban majalisar koli ta malaman darikar Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, tare da yi masa tambayoyi an kan rashin biyayya ga umarnin jiha na hana dukkan wani taro har na addini a jihar saboda gujewa kamuwa da kwayar coronavirus.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya shaidawa manema labarai, da yammacin ranar Talata, cewa sun gayyaci Sheikh Jingir zuwa hedikwatar saboda ya jagoranci magoya bayansa sallar Juma'a duk da an saka dokar hana taron jama'a.

A cewar ASP Gabriel, kwamishinan 'yan sandan jihar, Isaac Akinmoyed, ya shaidawa Sheikh Jingir cewa rundunar 'yan sanda ba zata lamunci irin wannan halin ba a jihar.

ASP Gabriel ya kara da cewa Sheikh Jingir, yayin da yake martani a gaban kwamishinan, ya dauki alkawarin yin biyayya ga dukkan umarnin gwamnatin jiha a kan yunkurin dakile annobar cutar covid-19.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa Sheikh Yahaya Jingir ya bayyana biyayyarsa ga gwamnatin jihar Filato, bayan tambayoyin da ya amsa daga wajen hukumar jami'an tsaro ta fararen kaya (DSS) a kan zarginsa da take dokar hana walwala a jihar don hana yaduwar muguwar cutar Coronavirus.

Rundunar 'yan sanda ta kira Sheikh Jingir don sake amsa tambayoyi a kan saba dokar jiha
Sheikh Jingir
Asali: Twitter

Idan zamu tuna, Jingir ya jagoranci jama'a masu tarin yawa don sallar Juma'a a masallacin Yantaya a ranar Juma'a da ta gabata, duk kuwa da umarnin gwamnatin jihar na hana taron da ya kai mutane 50.

Wata majiya mai karfi wacce ke da kusanci da Gwamna Simon Lalong ta tabbatar da cewa jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya sun gayyaci Sheikh Jingir.

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta daya a Najeriya ya bayyana tsirrai 2 da ke maganin cutar coronavirus

"An gayyaci babban malamin addinin don amsa wasu tambayoyi," majiyar ta sanar da wakilin jaridar Daily Nigerian.

Wata majiya ta kusa da hedkwatar jami'an tsaron fararen kayan ta kara tabbatar da cewa an tuhumi malamin. A cewar majiyar: "Manyan jami'ai daga babban ofishinmu na Abuja sun zo kuma sun gayyaci Sheikh Jingir a ranar Asabar da kuma Lahadi. An tuhume shi amma daga baya sai aka barshi ya tafi gida,"

A lokacin da aka tuntubi sakataren yada labarai na JIBWIS din, Ahmad Ashir ya ce bai san cewa an tuhumi shugaban nasu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel