Kin zuwan Shugaba Buhari Majalisa alamun mulkin karfa-karfa ne inji Ayo Fayose

Kin zuwan Shugaba Buhari Majalisa alamun mulkin karfa-karfa ne inji Ayo Fayose

- Ayo Fayose ya yi tir da watsin da Shugaban kasa ya yi da gayyatar Majalisa

- Tsohon Gwamnan yace dama ya san Buhari ba zai taba amsa gayyatarsu ba

- Fayose ya ce yanzu kowa na ta nadamar ba Muhammadu Buhari kuri’arsa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya soki shugaba Muhammadu Buhari a dalilin kin zuwansa zauren majalisar wakilan tarayya.

A cewar Ayo Fayose rashin zuwa majalisar kamar yadda aka bukata, rashin sanin martabar majalisa ne, wanda tubali ne a damukaradiyya.

“Na fada a ranar 1 ga watan Disamba cewa shugaban kasa Buhari ba zai amsa gayyatar majalisar wakilai domin bayani game da sha’anin tsaro ba.”

“Kuma haka aka yi, bai yi ba!” Inji Fayose.

KU KARANTA: An cigaba da shari'a da Fayose a kotu

“Idan kuna da shugaban kasa da aka zaba maras ganin darajar sauran bangarorin gwamnati, me ya wuce kace masa ban da mai karfa-karfa?”

Fayose wanda ya sauka daga kujerar gwamnan jihar Ekiti a 2018 ya yi wannan magana ne a shafinsa na sada zumunta, Twitter jiya da yamma.

Wani Bawan Allah ya maida martani ga fitaccen ‘dan adawar, yace an yi irin haka da tsohon shugaba, Dr. Goodluck Jonathan, shi ma ya tubure.

Ya ce: “Kafin 2015 da bayan nan, duk wadanda ba su goyon bayan abin da na fada game da Buhari sun gane gaskiya, sun yi kuskuren zaben shi.”

KU KARANTA: COVID-19 ta hada Fayose da Fayemi a rumfa daya

Kin zuwan Shugaba Buhari Majalisa alamun mulkin karfa-karfa ne inji Ayo Fayose
Ayodele Fayose Hoto; legit.ng
Asali: Original

“Ina ganin ya kamata su fito su ba jama’a hakuri na zuga ‘yan Najeriya da su ka sa aka zabe shi.

A ranar Alhamis aka sa ran ganin shugaban kasa ya hallara a majalisa domin yin bayanin abin da ke faruwa dangane da sha’anin tsaron kasa.

Bayan an gama magana, Mai girma Muhammadu Buhari ya lashe amansa, ya ki amsa goron gayyatar da ‘yan majalisar kasar suka aiko masa.

Gwamnoni da manyan jam'iyya su na cikin wadanda suka zuga Buhari ya ki amsa goron gayyatar majalisar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel