Zauren Arewa: Siyasa ita kadai ce babbar masana'antar Arewa

Zauren Arewa: Siyasa ita kadai ce babbar masana'antar Arewa

- ACF ta ce yaran arewa sun mayar da rikici hanyar samun nishadi

- Audu Ogbeh, shugaban ACF ya ce kullum tsaron arewa tabarbarewa yake yi

- Ya fadi hakan ne lokacin da ya kaiwa gwamna Zulum ziyara

Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya ce harkar tsaron arewa kullum tabarbarewa take yi. Ogbeh ya jagoranci mutane zuwa Maiduguri don jajanta wa gwamnan a kan kashe-kashen Zabarmari.

Fiye da manoma 40 'yan Boko Haram suka kashe a kauyen da ke karkashin karamar hukumar Jere a makonnin da suka gabata, The Cable ta wallafa.

Tsohon ministan ya ce babbar matsalar da ke addabar arewa shine yadda aka mayar da siyasa ta zama hanyar da kowa yake son ya samu kudi da ita. Ya kara da cewa siyasa kuwa bata samar da cigaba a ko ina.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce

Zauren Arewa: Siyasa ita kadai ce babbar masana'antar Arewa
Zauren Arewa: Siyasa ita kadai ce babbar masana'antar Arewa. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

"Muna cikin matsananciyar damuwa. Duk wanda a cikinmu baya cikin damuwa yanzu haka, bai haifu ba. Saboda ba mu da abinda za mu bai wa yaranmu, kuma rikici ba zai kai mu ko ina ba," kamar yadda wata takarda ta ranar Litinin ta yanko maganganun Ogbeh.

"Babbar matsalar da muke da ita shine ba mu da wata hanyar samu, in ban da siyasa. Kuma babu inda siyasa za ta kai wata al'umma.

"Dolene mu kara gina jihar Borno, mu gina arewa sannan mu gina Najeriya. Ba mu da wasu masana'antu, harkar noma ta lalace sannan yaran mu sun mayar da rikici da tashin hankali a matsayin hanyar samun nishadi," yace

KU KARANTA: Matashin likita tare da abokinsa sun kone kurmus a hatsarin mota a Katsina

A wani labari na daban, wani bidyo da yake nuna shugaban ma'aikatan fadar gwamna jihar Abia, Anthony Agbazuere yana zuba wa wani fasto mai suna Odumeje wanda aka fi sani da Indaboski ya janyo cece-kuce.

A bidyon da wani mai suna Enwagboso ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga Agbazuere yana watsa wa Chuwuemka Ohanaremere wanda aka fi sani da Odumeje kudi.

A bidiyon, ba a ga wacce rana lamarin ya faru ba, amma ya bayyana cewa a ofishin Agbazuerre ya faru, Channels Tv ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel